in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin tana nacewa ga manufar cudanya bisa tushen martaba juna
2018-12-11 19:13:23 cri

A yau Talata ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, har kullum kasar Sin tana nacewa ga manufar yin cudanya, da shawarwari ba tare da rufa rufa ba bisa tushen martaba juna.

Bisa labaran da kafofin watsa labaran kasar Jamus suka bayar, an ce, yayin ganawa tsakanin shugabannin kasashen Sin da Jamus a kwanan baya, shugaban Jamus ya tabo batun yanayin da kasar Sin ke ciki wajen kare hakkin dan Adam. Game da hakan, Lu Kang ya bayyana cewa, Sin da Jamsu suna gudanar da cudanya, da hadin gwiwa tsakaninsu yadda ya kamata, haka kuma suna cudanya kan kare hakkin dan Adama, da fuskantar kalubalen da ci gaban fasahohin zamani ke kawo wa kasashen duniya.

An ce, a ranar 10 ga wata, jakadan Amurka dake kasar Sin Terry Branstad, ya fitar da wata sanarwa kan ranar kare hakkin dan Adam, inda ya amince da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin kare hakkin dan Adam, amma a sa'i daya kuma, ya zargi kasar Sin da gazawa wajen kare hakkin dan Adam na al'ummun kasar. Bisa hakan ne kuma Lu Kang ya bayyana cewa, ya lura jakadan ya amince da sakamakon da kasar Sin ta samu a wannan fanni, sai dai yana fatan Amurkawa za su amince da hanyar raya kasa, da kare hakkin dan Adam da al'ummun kasar Sin suka zabawa kan su.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China