in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya yi bayani kan harkokin diflomasiyyar Sin a 2018
2018-12-11 19:04:49 cri

Ya zuwa karshen shekarar bana, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi cikakken bayani kan harkokin diflomasiyyar kasar Sin a shekarar bana, da kuma yin hasashe kan ayyukan diflomasiyya a shekara mai zuwa.

Yau Talata, Wang Yi ya halarci bikin bude taron karawa juna sani kan yanayin kasa da kasa da diflomasiyyar kasa ta Sin na shekarar 2018 a birnin Beijing, inda ya bayyana cewa, a shekarar 2018, kasar Sin ta ci gaba da aiwatar da ayyukan diflomasiyyarta bisa hanyar da ta tsara, duk da ta gamu da matsaloli da dama. Ya kuma yi bayani kan yadda kasar Sin take tafiyar da harkokin diflomasiyyarta da kalmomi guda shida, wadanda suka hada da, bude kofa ga waje, hadin gwiwa, ci gaba cikin zaman karko, jagoranci, sauke nauyinta da kuma tsayawa tsayin daka.

A farkon shekarar 2018, Sin ta sanar da manufarta ta kara bude kofa ga waje cikin taron dandalin Boao na kasashen Asiya. A yayin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kara bude kofa ga waje, sa'an nan ya gabatar da jerin matakan da abin ya shafa domin cimma wannan buri.

A yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko da aka yi a birnin Shanghai a watan Oktoba, jimilar kamfanoni 3600 daga kasashe, yankuna da kuma kungiyoyin kasa da kasa 172 ne suka halarci wannan biki. Kuma jimillar kudin ciniki da aka samar a yayin bikin ya kai yuan biliyan 60, lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin wajen kafa tsarin ciniki mai bude kofa ga waje. Wang Yi ya ce, kara bude kofa ga waje, shi ne babban aikin kasar Sin a fannin diflomasiyya a shekarar 2018, a cewarsa: "Yayin da ake fuskantar yaduwar ra'ayin kariyar ciniki, da na kashin kai da kuma cin zarafin a duniyarmu, kasar Sin a ko da yaushe na goyon bayan shirin dunkulewar duniya waje guda, da tsarin ciniki cikin 'yanci, gami da manufar ba bangarori daban daban damar shiga a dama da su. Tun daga farko shekarar bana har zuwa karshenta, a wajen bukukuwan hulda da kasashen waje da suka gudana a kasar Sin, da tarurukan kasa da kasa, kuma a duk bangarorin gabatar da manufofi da kuma daukar takamaiman matakai, kasar Sin na ta kokarin sanar da manufar kara bude kofarta, tana tsayawa tare da bangaren da ya nuna hangen nesa da sanin ya kamata."

Ko shakka babu, shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta riga ta zama shawarar da ta fi samun karbuwa a duniya, gami da wani dandali na gudanar da hadin gwiwa mafi girma. A cewar mista Wang Yi, manufar kasar Sin ta yin hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna, ita ce wadda ta fi janyo hankalin jama'ar duniya tsakanin manufofin hulda da kasashen waje da kasar Sin ta gabatar a shekarar 2018.

Kullum kasar Sin na tsayawa kan yin shawarwari kan manyan manufofin hadin kai, da kafa dandamalin hadin kai, da kuma more nasarorin da aka cimma wajen hadin kai, a maimakon bin umurnin wane bangare, da kuma tsayawa kan manufar bude kofa dake kunshe da kowa da kowa, a maimakon kafa karamar kungiya don neman moriya, kana tana tsayawa kan neman dauwamamman ci gaba ta hanyar kiyaye muhalli, da kuma bin dokokin kasa da kasa da na sauran kasashe.

Dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na jawo hankulan duniya. Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump a lokacin taron kolin kungiyar G20, inda bangarorin biyu suka amince da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka irin ta daidaituwa da hadin kai da kuma zaman karko, da nufin warware matsalolin dake akwai a tsakanin kasashen biyu, da tsara shiri kan ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba yadda ya kamata. Wang Yi ya jaddada cewa, kamata ya yi kasar Amurka ta yi watsi da ra'ayin na yin takara ba tare da samun moriya ba, kada ta tayar da takaddama, hakan za a bullo da sabon dan takara, ya ce: "Kawo yanzu, a huldar diplomasiyya dake tsakanin Sin da Amurka ta kai tsawon shekaru 40, a cikin wadannan shekarun, sassan biyu sun gamu da matsaloli daban daban, an lura cewa, idan sassan biyu suka hada kai, za su samu moriya tare, amma idan suka yi yaki da juna, tabbas za su gurgunta moriyarsu duka, a don haka ya dace masu hangen nesa na kasashen biyu su cimma matsaya guda kan batun rashin lalata moriyar juna, Amurka kuwa ya kamata ta daina yin takara ba tare da yin hakuri da juna ba, ta amince da ci gaban kasar Sin, haka kuma ta yi kokari tare da kasar Sin domin samun ci gaba tare, kada ta mayar da kasar Sin matsayin abokiyar gabarta."

Wang Yi ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, ana shiga lokaci mai muhimmanci wajen yin kwaskwarima kan tsarin kasa da kasa, da kuma raya tattalin arzikin duniya. Kasar Sin ta yi la'akari da yanayin zamani da ake ciki, da sa kaimi ga raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama, da kafa sabuwar dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da sa kaimi ga raya tsarin sarrafa duniya cikin adalci. A shekarar 2019, za a cika shekaru 70 da kafa sabuwar kasar Sin. Kasar Sin za ta gudanar da taron tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa masu bin shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" karo na biyu, da sa kaimi ga sada zumunta da yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen duniya, da tabbatar da zaman lafiya a yankin har ma a duniya baki daya, da kuma shiga aikin sarrafa duniya da gudanar da manufofin diplomasiyya na musamman dake dacewa da yanayin Sin a sabon lokaci.(Maryam Bello Bilkisu Jamila Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China