in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu babban ci gaba a fannin kare hakkin bil Adam cikin shekaru 70 da suka wuce
2018-12-11 14:58:01 cri





Ranar 10 ga watan Disamban kowa ce shekara rana ce ta kare hakkin bil Adam ta duniya, don haka, cibiyar nazarin kare hakkin bil Adam ta kasar Sin da asusun kare hakkin bil Adam ta kasar suka shirya taron cika shekaru 70 da bayar da sanarwar kare hakkin bil Adam a duniya, taron ya yi nuni da cewa, cikin shekaru 70 da suka wuce, kasar Sin ta samu gagaruman nasarori a fannin martaba da kare hakkin bil Adam.

A ranar 10 ga watan Disamban shekarar 1948 ne, aka zartas da sanarwar kare hakkin bil Adam ta duniya, sanarwar na da mutukar ma'ana ga kiyaye wayin kan al'umma. A yayin taron da aka gudanar a wannan rana, shugaban sashen kula da harkokin fadakarwa na kwamitin kolin na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin ya bayyana cewa, shekaru 70 da suka wuce shekaru ne da ke cike da manyan sauye-sauye, kuma cikin wadannan shekaru 70 da suka wuce, kasar Sin ta kama hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayin da take ciki tare da samar da ci gaban a zo a gani, haka kuma ta samu gagarumar nasara a fannin martaba da kare hakkin bil Adam. Ya ce,"Mun kare hakkin rayuwa da hakkin neman ci gaba na al'umma, har ma an kai ga kyautata yanayin da al'umma ke ciki matuka. Matsakaicin tsawon rayuwar al'umma ya karu zuwa shekaru 76.7 a shekarar 2017 kwatankwacin shekaru 35 kafin kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, a yayin da yawan al'umma da ke fama da jahilci ya ragu zuwa kimanin kaso 5% daga sama da kaso 80%. Sa'an nan, cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, kudin shigar al'ummar kasar Sin ya ninka har sau 22.8, a yayin da adadin al'ummar da ke fama da talauci ya ragu da miliyan 740, har ma an kai ga bullo da tsarin inganta rayuwar al'umma mafi yawa a duniya."

Ban da haka, ta fannin martaba da kare hakkin bil Adam, kasar Sin ta kuma kiyaye hakkin al'ummarta na kula da harkokin kasar, ta kuma bullo da tsarin dokokin kare hakkin bil Adam da ya dace da yanayin da kasar ke ciki. Chang Jian, zaunannen wakilin cibiyar nazarin kare hakkin bil Adam ta kasar Sin kana shugaban sashen nazarin kare hakkin bil Adam na jami'ar Nankai ta kasar ya ce, "Kasar Sin ta sanya batun kare hakkin rayuwa da kuma hakkin ci gaba a matsayin hakkoki na farko na bil Adam, kuma ta hanyar kiyaye hakkokin ne, aka yi nasarar kiyaye hakkin bil Adam ta sauran fannoni. Kasar Sin ta dora muhimmanci a kan kiyaye hakkin bil Adam na wasu rukunonin al'umma na musamman, musamman ma kananan kabilu da mata da yara da tsoffi da kuma masu nakasa. Ba kawai kasar Sin ke mai da hankali a kan batun kare hakkin bil Adam na daidaikon mutane ba, tana kuma mai da hankali a kan hakki na rukunonin jama'a, kuma tana tsayawa kan tabbatar da hakkinsu cikin daidaito. A game da sabanin da ake fuskanta ta fannin kare hakkin bil Adam, kasar Sin tana ganin cewa, ya kamata a daidaita shi ta hanyar yin shawarwari da juna. "

Duk da ci gaban da aka samu a fannin kare hakkin bil Adam, amma har yanzu akwai sauran rina a kaba. A halin yanzu, mutane sama da miliyan 700 a fadin duniya na fama da matsanancin talauci, a yayin da mutane sama da miliyan 132 ke matukar bukatar agajin gaggawa, sa'an nan, mutane sama da miliyan 65 sun rasa matsgunansu. Har yanzu ba a kai ga kawar da illolin da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya haifar kwata kwata ba, kuma kasashe masu tasowa na ci gaba da fuskantar rashin adalci. Har illa yau, rikicin shiyya shiyya da kuma ta'addanci na kawo barazana ga batun kare hakkin bil Adam a duniya. A game da wannan, Mr.Li Junhua, shugaban sashen kula da harkokin kasa da kasa na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi nuni da cewa, ba karamin aiki ba ne, idan har ana son a kai ga cimma burin da aka sanya gaba kamar yadda aka tanada cikin sanarwar kare hakkin bil Adam, a halin da ake ciki yanzu, ya kamata a hada karfi da karfe, don ciyar da aikin kare hakkin bil Adam a duniya baki daya gaba. Ya ce, "Na farko, ya kamata a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, na biyu ya kamata a kiyaye adalci da zaman daidai wa daida a duniya, na uku, ya kamata a kiyaye hakkin bil Adam a lokacin da ake kokarin neman ci gaban zamantakewar al'umma, na hudu, ya kamata a nace ga manufar ba da muhimmanci ga batun da ya shafi jama'a." (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China