in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Falasdinawa 32 sun jikkata sanadiyyar rikici tsakaninsu da sojojin Isra'ila a arewacin Gaza
2018-12-11 10:06:56 cri
Jami'an lafiya sun ce Falasdinawa masu zanga-zanga a kalla 32 ne suka jikkata, yayin rikicin da ya barke tsakaninsu da sojojin Isra'ila da aka girke kan iyakar dake tsakanin arewacin zirin Gaza da Isra'ila.

A cewar wata sanarwa da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta fitar, 11 daga cikinsu sun jikkata ne sanadiyyar harbi da harsasan bindiga na asali, yayin da 12 daga cikinsu suka samu rauni daga harsashin da aka lullube da roba, inda sauran 9 suka samu rauni daga gwangwanin hayaki mai sa hawaye.

A kowacce ranar Litinin, Falasdinawa masu zanga-zanga kan taru a kusa da bakin tekun dake arewacin zirin Gaza kusa da shingen iyakarsa da Isra'ila, suna masu kira da a dage shingen mai shekaru 12 da ya kange yankunansu.

Haka zalika, a kan yi wata zanga-zangar a duk ranar Juma'a, a wani gangami na neman dawo musu da yankunansu, wanda aka fara tun ranar 30 ga watan Maris.

Kungiyar Hamas da sauran kananan kungiyoyi dake Gaza, wandanda ke jagorantar gangamin, sun dage cewa ba za su daina ba har sai Isra'ila ta dage shingen. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China