in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta nada Tetteh ta kasar Ghana a matsayin babbar wakiliyar MDD a AU
2018-12-11 09:39:11 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres a jiya Litinin ya nada Hanna Serwaa Tetteh ta kasar Ghana a matsayin babbar wakiliyar MDD a kungiyar tarayyar Afrika AU.

Tetteh wadda ta maye gurbin Sahle-Work Zewde ta kasar Habasha a matsayin wakiliyar musamman ta babban sakataten MDD a AU, kuma shugabar ofishin MDD a wajen. Zewde ta bar aiki ne bayan da aka zabe ta a matsayin mace ta farko da za ta shugabanci kasar Habasha a watan Oktoban shekarar 2018.

Tetteh tana da kwarewar aiki na gwamman shekaru a matakin kasa, shiyya da kuma matakin kasa da kasa, ciki har da kwarewar aiki wajen dabarun samar da daidaito a tsakanin masu ruwa da tsaki, in ji ofishin yada labaran mista Guterres.

A halin yanzu tana shugabantar ofishin MDD a birnin Nairobi, Tetteh ta taba rike mukamin ministar harkokin wajen Ghana kuma mamba a majalisar tsaron kasar da majalisar dakarun sojojin kasar. Kafin haka ita ce ministar ciniki da masana'antun kasar ta Ghana.

Daga shekarar 2014 zuwa 2015 ita ce shugabar majalisar ministoci kuma shugabar majalisar sasanto a majalisar wanzar da tsaro na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China