in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya yi shawarwari da takwaransa na Jamus
2018-12-10 20:37:16 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, sun zanta a yau a babban dakin taron jama'a dake nan birnin Beijing, inda suka cimma matsaya daya cewa, kasashensu za su kara zurfafa fahimtar juna da hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za su ciyar da huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninsu gaba, ta yadda a karshe za su samar da moriya, da wadata, da zaman lafiya ga al'ummominsu, da kuma al'ummomin kasashen duniya baki daya.

Shugabannin biyu sun kara da cewa, za su hada kai domin gudanar da harkokin kasa da kasa yadda ya kamata, tare kuma da raya tattalin arzikin duniya ba tare da rufa rufa ba, kana sun bayyana cewa, za su yi kokari tare domin kiyaye tsarin cinikayya maras shinge, da tabbatar da yarjejeniyar dakile matsalar sauyin yanayi ta Paris, da tsarin dake tsakanin bangarori daban daban karkashin jagorancin MDD.

A nasa bangare, Frank-Walter Steinmeier ya yabawa kasar Sin, saboda sakamakon da ta samu tun bayan da ta fara aiwatar da manufar gyaran fuska da bude kofa kafin shekaru 40 da suka gabata, musamman ma a fannin yaki da talauci. Ya ce, kasarsa tana son kara karfafa tattaunawa da kasar Sin domin kara fahimtar juna, da kuma zurfafa hadin gwiwa.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China