in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar wakilan kwamitin koli na JKS ta isa Guangxi domin taya lardin murnar cika shekaru 60 da kafuwa
2018-12-10 19:25:38 cri

Tawagar wakilan kwamitin koli na JKS karkashin jagorancin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Wang Yang, ta isa lardin Guangxi domin taya al'ummar sa murnar cika shekaru 60 da kafuwa.

Tawagar ta isa birnin Nanning, fadar mulkin lardin ne a jiya Lahadi, inda ta mikawa mahukuntan sa wani allon sanarwa mai dauke da wani rubutu na shugaban kasar Sin, kuma babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping.

A kan allon dai an rubuta wani sako dake cewa "Gina lardin Guangxi mai ban sha'awa da kayatarwa, aikin hadin gwiwa ne da ya tabbatar da mafarkin farfadowa da ya zama gaskiya."

Da take tsokaci yayin isar tawagar lardin, mamba a hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS Sun Chunlan, ta ce shugaban kasar Sin Xi Jinping na martaba daukacin kabilun dake lardin Guangxi.

Ta ce kalaman da shugaba Xi ya rubuta a allon sanarwar da suka gabatar, na nuni da irin fatan alheri, da muhimmin burin da shugaban na Sin yake da shi a kan lardin na Guangxi, kuma hakan zai kara zaburar da al'ummar lardin wajen kara kwazon aiki, tare da tunkarar nasarar zamanantar da al'ummar kasar Sin baki daya cikin hadin gwiwa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China