in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Bai kamata a rika hada hakkin bil Adam da manufar siyasa ba
2018-12-10 18:45:47 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana cewa, kamar yadda sauran kasashe masu tasowa suke yi, kasar Sin tana adawa da hade manufar siyasa da hakkin bil Adam, kuma bai kamata a rika amfani da ma'auni iri biyu ba.

Yau ce dai ranar kare hakkin dan Adam ta duniya, kuma kawo yanzu ana ci gaba da fuskantar sabani tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba a fannin kare hakkin bil Adam.

Game da yadda za a gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a wannan fannin, Lu Kang bayyana cewa, "Ingiza aniya da kare hakkin dan Adam buri ne na daukacin bil Adam, don haka ya kamata kasashen duniya su yi amfani da wannan dama ta tunawa da ranar kare hakkin bil Adama, domin kara karfafa aikin kare hakkin bil Adam, tare kuma da sa kaimi kan cudanya a fannin bisa tushen ka'idojin MDD. Sai dai kuma a cewar sa, ya dace a yi himmar kawar da duk wani sabani ta hanyar yin shawarwari."

Ya ce, kasar Sin tana son kara karfafa cudanya da hadin gwiwa a fannin kare hakkin bil Adama tsakaninta da sauran kasashen duniya, bisa tushen daidaito da martaba juna, ta yadda za su samu ci gaba tare cikin lumana.

Jami'in ya yi wannan tsokaci ne a Litinin din nan, yayin taron ganawa da manema labarai da aka saba yi a nan birnin Beijing.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China