A cewar shugaban, jama'ar kasar Sin na son yin hadin gwiwa da jama'ar sauran kasashe, a kokarin tabbatar da zaman lafiya, da samun ci gaba, da daidaito, da adalci, da tsarin dimokuradiyya, gami da 'yancin dan Adam. Ban da wannan kuma za a kare mutunci, da hakkin kowane bil-Adam a fannoni daban daban, da kokarin bullo da tsarin kare hakkin dan Adam mai adalci, da hakuri da ra'ayoyi daban daban, ta yadda za a raya al'ummar bil Adama mai makomar bai daya, da tabbatar da samar da yanayi mai kyau a duniyarmu. (Bello Wang)