in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Canada ta zama matattarar garkuwa da mutane ta fuskar siyasa
2018-12-10 12:31:44 cri

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Le Yucheng ya bukaci jakadan Canada a kasar Sin John McCallum a ranar 8 ga watan Disamba, inda ya bukaci a gaggauta sakin babbar jami'ar kudi ta kamfanin Huawei, Meng Wanzhou, wadda aka tsare ta a lokacin da yake kokarin sauya jirgin sama a Vancouver bisa ga umarnin da gwamnatin Amurka ta bayar.

Kasar Canada tana zumudin kasancewa a sahun gaba don zama wata matattarar yin garkuwa da mutane a siyasance, tana kokarin bayyana halayyarta ga masu bibiyar al'amurran kasa da kasa.

A wasu 'yan watanni da suka gabata, firaiministan kasar Canada Justin Trudeau ya fito fili karara inda ya soki gwamnatin Amurka bisa abin da ya kira cewa Amurkar tana yunkurin buga haraji kan karafa da sanholo da ake shigarwa kasarta inda take fakewa da dalilai na tsaron kasa: Mu 'yan kasar Canada, muna da saukin mu'amala, muna da tunani, amma ba za mu taba yarda a juya mu yadda aka ga dama ba." Kasarsa ta kaddamar da wasu jerin matakai na daukar fansa, ciki har da kai Amurka kara gabatan kwamitin kungiyar ciniki ta duniya WTO, da buga harajin kashi 25 bisa 100 na kayayyakin da Amurka ke shigarwa kasarta wanda aka kiyasta kudinsu dala biliyan 12.6, matakin ya fara aiki a ranar 1 ga watan Yuli. Al'ummar kasa da kasa sun yabawa kasar Canada bisa wannan jajurcewa da ta nuna domin kare moriyarta.

To sai dai kuma, kasar ta Canada wadda ta nuna cewa "ba za'a juya ta yadda aka ga dama ba" sai ga shi tana kokarin nuna halin rashin dattaku "ana amfani da ita": sakamakon yadda ta tsare babbar jami'ar kamfanin Huawei bayan da Amurka ta umarce ta da yin hakan, wannan batu ya kasance abin takaice kuma abin kunya ga kasashen biyu.

Wani marubuci na babbar jaridar kasar Canada, the Globe and Mail, Alex Duhaney a birnin Ottawa ya rubuta cewa: "Na ji matukar kunya kasancewar gwamnatinmu ta shigar da kanta aikin yin garkuwa da neman kudaden fansa na wata babbar jami'ar kamfanin kasar waje. Wannan mataki ya haifar da zubewar mutunci da kimar gwamnati mai ci, kuma ya jefa rayuwar jama'ar Canada dake harkokin kasuwanci a kasashen waje cikin hadari."

Shi ma wani marubucin a Victoria, British Columbia da ake kira Larry Hannant, ya rubuta cewa: "A kwanan nan gwamnatin Trump ta bada umarni duk da kin amincewar kwamitin sulhun MDD, game da batun hukunta Iran wanda duniya ta yi Allah wadai da shi. A maimakon yin abin da ya dace, sai kasar Canada ta yi gabatan kanta wajen yin shisshigi kan takaddamar da ta shafi kasa da kasa har ta taka rawa da bazar wata gwamnati mai nuna fifita kanta wajen yunkurin ruruta wutar rikici a tsakanin kasashen duniya."

A watannin baya bayan nan, gwamnatin kasar Canada, tana neman fadada harkokin cinikayyarta, tana yawan tuntubar bangaren kasar Sin domin cimma matsaya wajen karfafa mu'amalar cinikayya cikin 'yanci tsakanin kasashen biyu. Bayan Canada, Mexico da Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyar NAFTA 2.0, akwai rahotanni da dama da kafafen yada labarai suka watsa kan wannan batu da ake kira da suna "kwayar guba" wato "poison pill" a Turance, tsarin wanda Amurka ce ta gabatar da shi, a don haka ministar harkokin wajen Canada Chrystia Freeland ta bukaci takwaranta na kasar Sin Wang Yi, inda ta jaddada aniyar kasar Canada na shiga tattaunawa domin cimma matsaya game da tabbatar da kafa yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci tare da sauran kasashe. Sama da kwararrun kasar Canada 70 ne suka rubuta rahotanni game da yadda za'a warware matsalar ta "poison pill" da kuma yadda za'a kyautata mu'amalar ciniki da tattalin arziki tsakaninta da kasar Sin. A watan jiya, ministan kudin Canada Bill Morneau, da ministan huldar cinikayyar kasa da kasa na Canadan Jim Carr, sun ziyarci birnin Beijing, domin halartar taron tattauna dabarun bunkasa tattalin arziki da harkokin kudi na kasashen Sin da Canada irinsa na farko, wanda aka karbi bakuncinsa bisa hadin gwiwa da babban jami'in majalisar kasar Sin Wang Yong. Gwamnatin Canada daga bisani ta bayyana cewa "bangarorin biyu sun tabbatar da kudurinsu na zurfafa mu'amalar ciniki da fadada huldar tattalin arziki a tsakaninsu."

To sai dai kuma, duk da irin wadannan yunkurin na hadin gwiwa, sai ga shi batun yana neman zama karkashin alamar tambaya, sakamakon yadda Canada ta kama wata babbar jami'ar kasuwancin kasar Sin. Gordon Houlden, daraktan cibiyar kasar Sin a jami'ar Alberta, ya ce "baki dayan al'amarin wani mummunan labari ne a gare mu. Damar da gwamnatin Canada ke da ita na baiwa kamfanin Huawei damar aiwatar da fahasar nan ta 5G a wannan kasar a yanzu ta koma tamkar karamar dama ce. Amurka ba za ta taba amincewa da hakan ba. Ita ma kasar Sin, akwai yiwuwar ba za ta amince da tsarin yarjejeniayr cinikayyar bangare guda ba bisa manufar kasar Canada." Za'a iya cewa masu amfani da intanet a Canada sun shiga hali mai wuya, sakamakon yadda tsarin fasahar 5G mai saukin kudi zai iya shiririncewa. Ya kamata kotunan shari'a a Canada da gwamnatin kasar su yi kaffa kaffa domin kada wasu 'yan siyasa su yi amfani da su wajen mayar da su masu yin garkuwa da mutane a siyasance wanda babban burinsu shi ne lalata mu'amalar ciniki a tsakanin sauran kasashen duniya. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China