in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare Janar na MDD ya isa Morocco don halartar taron kasashen duniya kan kaura
2018-12-10 09:37:50 cri
Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya isa birnin Marrakech na Morocco a jiya Lahadi, domin halartar taron gwamnatocin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kaura ta MDD.

Bisa yadda aka tsara, taron zai amince da yarjejeniyar da aka cimma kan batun kaura a hukumance, wadda kasashe mambobin majalisar suka fara amincewa da ita a ranar 13 ga watan Yulin.

A cewar MDD, yarjejeniyar cikakken daftari ne da ya kunshi yadda za a lura da batun kaura a duniya, da yadda za a shawo kan kalubalenta da karfafa hakkokin masu kaura da kuma bada gudunmuwa ga samun ci gaba mai dorewa.

Wannan ita ce yarjejeniya ta farko da aka tsara karkashin inuwar MDD, domin ta mamaye kowanne bangare na batun kaura a duniya bisa yanayin da ya dace. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China