Sanarwar ta ce, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta ce, harin da aka kai da makamai masu guba da aka kaddamar a karshen watan Nuwamba na bana a Aleppo dake arewacin kasar Syria, ba dakaru masu adawa da gwamnatin Syria ne suka yi ba, sai dai sojojin gwamnatin Syria ne suka yi amfani da barkonon tsohuwa. Kasar Amurka ta yi wannan bayani ne da nufin wankewa dakaru masu adawa da gwamnatin Syria daga laifin da suka aikata, da kuma sanya kasashen duniya su rage maida hankali kan boma-boman da kasar Amurka ta harba a gabashin kasar Syria, wadanda suka haddasa rasuwar fararen hula da rautata wasu.
Kafofin watsa labaru na Syria sun bayar da labari a ranar 24 ga watan Nuwamba cewa, dakaru masu adawa da gwamnatin sun yi amfani da makaman roka masu guba don kai farmaki kan matsugunai da tituna na Aleppo, wannan ya sanya wasu fararen hula da dama suka kasa numfashi, ciki har da mata da yara. Bayan faruwar lamarin, sojojin gwamnatin kasar sun mayar da martani kan wurin da dakaru masu adawa da gwamnatin suka harba makaman roka. (Bilkisu)