in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don inganta yunkurin siyasar Syria
2018-12-08 17:17:42 cri
Manzon musamman na gwamnatin kasar Sin dake kula da batun kasar Syria Xie Xiaoyan ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai don ciyar da yunkurin siyasa a kasar ta Syria gaba.

Xie ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da manema labaru a jiya Juma'a a birnin Geneva, inda Xie ya kara da cewa, game da batun Syria, kullum kasar Sin na tsayawa kan warware matsaloli ta hanyar siyasa, kuma tana goyon bayan MDD da ta taka muhimmiyar rawa wajen yin sulhu, da nuna goyon baya ga manzon musamman na babban sakataren MDD kan kokarin da yake yi.

Xie ya bayyana cewa, yanzu an samu sassauci kan yanayin jin kai da kasar Syrian ke ciki, wasu 'yan gudun hijira ma sun soma komawa gidajensu, bangarorin da abin ya shafa sun soma tattaunawa kan sake raya kasar. Koda yake, har yanzu 'yan ta'adda suna tayar da tashin hankali, hakan na kawo barazana ga shiyyoyi da kasashen duniya, amma duk da haka an samu babbar nasara wajen yaki da ta'addanci. Bisa wannan yanayin da ake ciki, kamata yayi bangarori daban daban su yi amfani da wannan damar don inganta warware batun Syria a siyasance.

Xie ya kai ziyara a kasar Amurka da hedkwatar MDD dake New York a kwanan baya, ya kuma gana da manzon musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China