"hukumar CERF, ba kawai ya kasance a matsayin asusu mafi saurin samar da tallafi ga mutanen da rikici ya afka musu ba ne, har ma ya kasance a matsayin wani muhimmin asusu dake samar da ayyukan jin kan bil adama a duniya baki daya," inji babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya bayyana hakan a lokacin bude taron gidauniyar neman tallafin kudaden.
Asusun wanda babban taron MDD ya kafa shi a shekarar 2005, ya kasance daya daga cikin muhimman hanyoyin dake samar da taimako akan lokaci da kuma aikin ceton rayukan al'umma, yana sahun gaba wajen yin hadin gwiwa don samar da taimakon gaggawa na jin kan bil adama.
Tun bayan kafa shi, asasun ya tallafawa miliyoyin mutane a kasashen duniya da yankuna sama da 100 da kudaden da ya zarta dalar Amurka biliyan 5.5, a sakamakon kokari na bangarori masu bada tallafi da masu tallafawa ayyukan hukumar ba tare da nuna gajiyawa ba.