in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta harba na'urar Chang'e-4 don binciken duniyar wata
2018-12-08 16:27:21 cri

Da safiya yau Asabar ne kasar Sin ta harba na'urar Chang'e-4 domin yin aikin bincike a duniyar wata, ana saran na'urar zata isa duniyar watan a karon farko domin gudanar da bincike a bangare mai nisa na watan.

An yi amfani da samfurin Long March-3B roket, wajen daukar na'urar binciken don harbawa zuwa duniyar wata, wanda aka gudanar da aikin harbawar a cibiyar harba tauraron dan adam ta Xichang dake kudu maso yammacin kasar Sin a lardin Sichuan da misalin karfe 2:23 na safe, matakin da ya bude wani sabon babi a bangaren ayyukan bincike a duniyar wata.

Kasancewar yadda wata ke zagaya duniya yayi daidai da yadda yake juyawa, wani bangare na wata yake fuskantar duniyarmu a kullum. Don haka, yawanci ba za'a iya kallon bangare na daban na watan ba, kuma ana kiran wannan bangare mai nisa ko kuma mai duhu, ba wai saboda duhunsa ba, sai dai babu wani takamamman ilmi game da hakan.

Aikin na'urar ta Chang'e-4, zai kasance wani muhimmin mataki wajen bayyana yadda wannan bangare mai nisa na watan yake, inda babu wani takamamman ilmi game da shi a halin yanzu.

Sai dai kuma, saukar na'urar da yadda zata dinga jujjuyawa yana bukatar wani nau'in tauraron dan adam wanda zai dinga samar da bayanai game da aikin na'urar.

Don haka, kasar Sin ta harba tauraron dan adam na "Queqiao",wanda ake kira Magpie Bridge, tun a ranar 21 ga watan Mayu domin samar da wata hanyar samun bayanai tsakanin duniya da kuma bangaren duniyar watan.

Kasar Sin ta bayyana na'urar "Chang'e" a matsayin ta binciken duniyar wata, shirin kasar Sin na binciken wata ya fara ne tun a shekarar 2004, wanda ya hada da harbawa da kuma saukar na'urorin binciken duniyar wata, da kuma samo samfura daga duniyar watan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China