in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farashin man fetur ya fadi yayin da taron OPEC ya tashi ba tare da cimma yarjejeniyar rage yawan man da ake samarwa
2018-12-07 11:35:49 cri

Farashin man fetur a jiya Alhamis, ya yi fadi sosai yayin da kungiyar kasashe masu fitar da man fetur wato OPEC, ta kammala taronta ba tare da cimma matsaya game da yawan man da za a rage samarwa ba.

Kungiyar da Saudiyya ke jagoranta da kawayenta, sun gudanar da taro a hedkwatarta dake Vienna na kasar Austria, domin kokarin daidaita faduwar farashin man, yayin da ake tsaka da sa ran cimma yarjejeniyar rage yawan man da kasashen ke samarwa.

Rahotanni na cewa, OPEC ta amince ta rage man da ake samarwa, sai dai ba a bayyana yawan man da ta tsara janyewa daga kasuwa ba. Kungiyar ta shirya gudanar da wani taro da kawayenta ciki har da Rasha a yau Jumma'a.

Sai dai kuma, wani rahoton da hukumar bada bayanai kan makamashi na Amurka ta fitar a jiya, ya ce a makon da ya gabata, kasar ta kara yawan man da take fitarwa, inda adadin da ya kai ganga miliyan 3.2 a kowacce rana. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China