in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Kasar Sin ta yi kira da a samar da moriya ga kasashe daban-daban a duniya
2018-12-06 19:28:06 cri

A yau ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dawo gida birnin Beijing, bayan kammala ziyarar da ya kai a wasu kasashen Turai da na Latin Amurka guda hudu tare da halartar taron kolin kungiyar G20 a birnin Buenos Aires na kasar Argentina. A yayin da yake kasar Portugal, Xi ya bayyanawa kafofin watsa labarai cewa, ziyarar ta sa ya kara fahimtar kyakkyawan fatan jama'ar kasashe daban-daban na shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya, da neman bunkasuwar kasa da kasa da kuma jin dadin zaman rayuwarsu na yau da kullum.

Shugaba Xi ya ce, duk da matsaloli da kalubale daban-daban dake addabar duniya baki daya, amma kasarsa za ta himmatu tare da sauran kasashe don raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya bisa tushen girmama juna da yin shawarwari da juna gami da kawowa juna moriya.

Idan muka kalli ziyarar shugaba Xi a wannan karo, za mu fahinci cewa kasar Sin ta yi abin da ta saba yi a baya a wasu fannoni uku, wato, na farko, kamar yadda ta yi a da, Sin ta saurari ra'ayoyin kasashe daban-daban a wannan karo da kuma yin shawarwari da su don taimaka musu wajen daidaita matsaloli, na biyu, kamar yadda ta yi a baya, Sin ta bullo da shirye-shiryenta don goyon-bayan ra'ayin kasancewar kasashe daban-daban da inganta hadin-gwiwa tsakaninsu, na uku wato na karshe shi ne, kamar yadda ta yi a da, shugaban kasar Sin ya nuna matukar hangen nesa da daukar nauyin dake wuyansa. Duk wadannan al'amura sun taimaka sosai ga ci gaban kasashen duniya yayin da ake fuskantar abubuwa masu sarkakkiya a halin yanzu.

Halartar taron koli na G20 yana daya daga cikin muhimman ayyuka da shugaba Xi ya yi a yayin ziyarar tasa. Bana shekaru 10 ke nan da barkewar matsalar kudi ta duniya da soma gudanar da tsarin taron koli na G20. An kira taron koli na wannan karo ne a wani muhimmin lokaci kan tattalin arzikin duniya, a don haka ya jawo hankulan mutane sosai. A ranar da aka bude taron, shugaba Xi ya ba da muhimmin jawabi, bayan bikin rufe taron kuma, aka yi shawarwari a tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka, lamarin da ya fi jawo hankulan duniya baki daya.

A jerin shawarwari na bangarori biyu ko da dama, a matsayinsa na shugaban kasa mai tasowa da ta fi girma a duniya, shugaba Xi ya gabatar da jawabi a madadin kasashe masu tasowa, da tattara ra'ayin bai daya bisa ra'ayin kasancewar kasashe daban-daban a dukkan fannoni. Kana ya gabatar da cewa, dole ne a tsaya kan manufofi uku wajen gudanar da cinikayyar duniya, wato bude kofa, yin hakuri da kuma bisa ka'idoji, a cewarsa ya kamata a ba da muhimmanci ga batun neman ci gaba a yayin da ake tafiyar da tattalin arzikin duniya, da tsayawa kan hadin kai mai salon bude kofa, da raya abokantaka, da yin kirkire-kirkire da kuma samar da gajiya ga kowa da samun nasara tare, kana da inganta dangantakar dake tsakanin manyan kasashe yadda ya kamata. Wadannan jawaban da shugaba Xi ya yi sun samu amincewar kasashen duniya.

A karshen shekarar 2018, sanadiyar ziyarar shugaba Xi ya jaddada raya shawarar "Ziri daya da hanya daya", da zurfafa dangantakar abokantaka, da kuma sa himma wajen shiga ayyukan tafiyar da harkokin duniya. Ko shakka babu, akwai bukatar shugabanni da dama su sauke nauyin dake bisa wuyansu a wannan yanayi da duniya ke fuskantar sauye-sauye. (Murtala Zhang, Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China