in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta zama wani muhimmin bangare na ci gaban sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta duniya
2018-12-06 12:34:09 cri

Kamfanin Euroconsult, wanda ya kasance a matsayin wata hukuma mai fada a ji a duk fadin duniya a fannin nazarin kasuwar taurarin dan Adam, ya bayar da rahoto a birnin Beijing a jiya 5 ga wata, inda ya yi hasashen yanayin ci gaban sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta duniya nan da shekaru biyar masu zuwa, da nazarin bukatun kasuwar a nan gaba, da ma kimanta makomar sana'ar ba da hidima ga taurarin dan Adam.

Rahoton ya bayyana cewa, sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasuwanci ta duniya, za ta ci gaba da karuwa nan da shekaru biyar masu zuwa. A cikin wannan sana'a, kasar Sin tana bunkasuwa yadda ya kamata, har ma ta zama wani muhimmin bangare na ci gaban sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta duk duniya.

Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 40, tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida. A cikin wadannan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta samu manyan nasarori ta fuskar zirga-zirgar sararin samaniya. Kamar kara samun ci gaban aikin binciken duniyar wata, da shigar da tsarin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam kirar "Beidou" cikin irin tsarin na duniya, da kaddamar da amfanin tauraron dan Adam mai hango abubuwan da ke doron kasa, da ma habaka girman sana'ar taurarin dan Adam na sadarwa.

A yayin taron dandalin tattaunawa kan ci gaban zirga-zirgar sararin samaniya na duniya karo na shida da aka kira jiya a birnin Beijing, shugaban kamfanin Euroconsult Pacome Revillon ya bayyana cewa, yanzu haka kasar Sin na zama wani muhimmin bangare na ci gaban zirga-zirgar sararin samaniya na duniya. Yana mai cewa,

"Makwanni biyu da suka gabata, mun bayar da rahoton sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin. Ina ganin cewa, sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar Sin na samun saurin ci gaba, musamman a fannonin kirkire-kikiren kimiyya da fasaha, da yawan taurarin dan Adam da ya harba, da ma ci gaban tsarin sana'ar taurarin dan Adam. Bugu da kari, yanzu kasar Sin na kokarin hada kanta da dimbin hukumomin sama jannati na kasa da kasa, lamarin da ya sa kasar Sin ta kara samun yalwatuwa a fannin hadin gwiwa tare da kasashen waje. A waje daya kuma, yadda matasan kasar Sin ke zura ido kan sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ya burge ni sosai."

A 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin ta karfafa kwarin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu, wajen sa hannu cikin sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya, hakan ya sa sana'ar ta fuskar kasuwanci ta samu bunkasuwa, har ma an riga an samu cikakken tsarin sana'ar daga dukkan fannoni. He Xing, mataimakin shugaban rukunin masana'antu na Great Wall na kasar Sin ya furta cewa,

"kamfanonin zirga-zirgar sararin samaniya na gargajiya, da sabbin kamfanoni, da masu son zuba jari, dukkansu suna goyon bayan ci gaban sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasuwancin Sin. Yanzu kamfanonin zirga-zirgar sararin samaniya na kasuwanci na kasarmu sun kusan shafi dukkan fannonin tsarin sana'ar, wadanda suka hada da yin fasalin taurarin dan Adam, da nazarin roka da harbanta, da amfani da taurarin dan Adam da ke bin hanyoyinsu a kasuwa. Tauraron sadarwar na tafi-da-gidanka da ke kusa da duniyar bil Adama, da rukunin jerin taurarin dan Adam masu hango abubuwan da ke doron kasa, da tsarin karfafa amfanin jagorancin zirga-zirga ta hanyar tauraron dan Adam, da dai sauran manyan ayyukan zirga-zirgar sararin samaniya na kasuwanci, suna kara azama ga ci gaban sana'ar baki daya, wandanda su ma na kyautata tsarin sana'ar yadda ya kamata."

Bisa kididdigar da aka fitar, an ce, jimillar tattalin arzikin duniya da aka samu ta sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya a bara, ta kai dala biliyan 383.5 cikin jimillar ta kasuwanci ta zarce dala biliyan 308, lamarin da ya sa sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasuwanci ta fi ba da gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya.

Ban da wannan kuma, Mr. Pacome ya ba da shawarar cewa, nan gaba sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasuwancin kasar Sin, za ta shiga cikin kasuwar duniya sannu a hankali, a maimakon mai da hankali kan kasuwar cikin gida da take yi yanzu. Yana mai cewa,

"Sana'ar zirga-zirgar sararin samaniya ta kasuwancin kasar Sin ta fara bunkasa ba da dadewa ba, wadda ke da makoma mai haske. Domin kara saurin karuwar yawan kamfanonin zirga-zirgar sararin samaniya masu zaman kansu na kasar Sin, ya kamata a kokarta wajen neman abokan kasa da kasa don bude kasuwar duniya. Wannan sana'ar ta fi samun saurin ci gaba a kasashen Turai, da Amurka, da Rasha, da ma Japan, da ma ita kanta kasar Sin." (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China