Ma Zhaoxu ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin mahawarar da kwamitin tsaron MDD ya gudanar. Ya ce akwai bukatar dora muhimmancin gaske a fannonin samar da ci gaba, da tsaro, da yaki da fatara, matsalolin da akasarinsu ne ke haifar da tashe tashen hankula a sassan duniya.
Kaza lika jami'in ya yi kira ga kasashen duniya da su rika sauke nauyin dake wuyan su, na aiwatar da ajandar MDD ta wanzar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa domin samar da ci gaba, da karrama ayyukan tallafi, domin wanzar da zaman lafiya yadda ya kamata. Jami'in ya yi nuni ga tasirin manufar MDD ta shekarar 2015, wadda ta tanaji aiwatar da wasu kudurorin ci gaba 17 nan da shekarar 2030.
Har ila yau, wakilin na Sin ya ja hankalin kasashen duniya, da su tallafawa kasashe masu yunkurin farfadowa bayan fuskantar tashe tashen hankula da dabarun aiwatar da manufofin su, bisa yanayi da kuma ikon su na aiwatar da matakai bisa radin kan su. (Saminu Alhassan)