in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tana shirin samar da taimakon jin kai ga mutane miliyan 93.60 a 2019
2018-12-05 10:35:47 cri

A ranar 4 ga wata, mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin samar da taimakon jin kai Mark Lowcock ya bayyana a birnin Geneva cewa, za a ci gaba da shan aikin samar da taimakon jin kai a shekarar 2019 dake tafe, a don haka MDD tana shirin tattara taimakon kudin da yawansa zai kai dalar Amurka biliyan 25 domin samar da tallafin jin kai ga mutane miliyan 93 da dubu 600.

A dai wannan rana, MDD ta fitar da wani rahoto game da shirin samar da taimakon jin kai da za a aiwatar da shi a fadin duniya a shekarar 2019 mai zuwa, inda mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin samar da taimakon jin kai Mark Lowcock ya bayyana cewa, a shekarar dake tafe, wasu kasashe za su ci gaba da fama da tashe-tashen hankali, a don haka ana bukatar taimakon jin kai matuka, a cewarsa: "A shekarar 2019, ana ci gaba da bukatar taimakon jin kai matuka, mutane miliyan miliyan 132 dake kasashe 42 a fadin duniya suna bukatar taimakon jin kai. Yawancinsu suna rayuwa ne a cikin kasashen dake fama da tashe-tashen hankali cikin dogon lokaci, abu mai bakanta rai shi ne, ba bu wani ci gaba a bayyane da muka samu, a fannin kawar da wadannan rikice-rikice."

An ce, ana sa ran MDD za ta cimma burin tattara taimakon kudin da yawansa zai kai dalar Amurka biliyan 21 da miliyan 900, idan an hada kudin da kudin da ake samarwa kasar Syria, gaba daya adadin zai kai dala biliyan 25. Ya zuwa tsakiyar watan Nuwamban bana, MDD ta riga ta samu dala biliyan 13 da miliyan 900, adadin da ya karu da kaso 10 bisa dari idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara. Bisa shirin da aka tsara, MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa, suna shirin samar da taimakon abinci, da wurin kwana, da kiwon lafiya, da ba da ilmi ga mutane miliyan 93 da dubu 600 a shekarar 2019.

Mark Lowcock ya ce, a shekarar bana, adadin taimakon kudin da aka samu ya riga ya kai dala biliyan 22, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi. Ana iya cewa, an riga an samu babban sakamako a fannin samar da taimakon jin kai ga masu bukata.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, adadin mutanen dake bukatar taimakon jin kai yana karuwa a kai a kai, a don haka ana bukatar karin kudi, wato tsakanin shekarar 2014 zuwa shekarar 2018, adadin taimakon kudin da aka samar wa kasashen Somaliya, da Sudan ta Kudu, da Sudan, da Syria, ya kai kaso 55 bisa dari dake cikin daukacin kudin taimakon da aka samar. Mark Lowcock ya bayyana cewa, a shekarar 2019, kasar Yemen ita ma tana bukatar taimakon jin kai, ya ce: "Babbar matsalar da muke fuskantar a shekarar 2019 ita ce kasar Yemen, mun yi hasashen cewa, kaso 75 bisa dari na mutanen kasar su miliyan 24, suna bukatar taimakon jin kai. Yanzu haka MDD tana kokarin samar da taimako ga mutum miliyan 15 daga cikinsu, muna fatan adadin taimakon kudin da za mu samar wa kasar zai kai dala biliyan 4."

A karshe dai Mark Lowcock ya jaddada cewa, nan gaba ya dace a kara mai da hankali kan dalilan da za su haifar da rikicin jin kai, yana mai cewa, "Na yi nazari sosai kan yanayin samar da taimakon jin kai da muke ciki a shekarar bana, yanzu na lura cewa, akwai bukata mu kara mai da hankali kan dalilan da suke haifar da rikicin jin kai. Alal misali tashe-tashen hankula, da talauci, da sauyin yanayi da sauransu, shi ya sa za mu mayar da aikin a matsayin mafi muhimamnci a shekarar 2019 dake tafe."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China