in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Portugal
2018-12-05 09:48:04 cri

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Portugal Marcelo Rebelo de Sousa. A yayin ganawar tasu, shugabannin biyu sun cimma ra'ayi daya, wajen mai da shekarar cika shekaru 40 da kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, a matsayin wani sabon mafari na inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, domin bude wani sabon shafi na zumuncin dake tsakanin Sin da Portugal.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana fatan kasashen biyu za su nuna goyon baya ga juna kan harkokin dake shafar babbar moriyar su, da kuma ci gaba da mu'amalar dake tsakanin manyan jami'an kasashen biyu, domin zurfafa zumuncin siyasa a tsakanin kasashen biyu. Sa'an nan, ya kamata kasashen biyu su kara hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa tsarin "Ziri daya da hanya daya", domin inganta musayar kasashen biyu a fannoni daban daban.

Haka zalika, shugaba Xi ya ce, ana fatan kasashen biyu za su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin habaka musayar ciniki, yayin da ake karfafa mu'amalar dake tsakaninsu kan manyan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a kiyaye 'yancin ciniki yadda ya kamata.

A nasa bangare kuma, Marcelo Rebelo de Sousa ya ce, kasar Portugal tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin, a fannin tattalin arziki da cinikayya, da sha'anin kudi, da raya al'adu da dai sauransu. Kuma yana maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin kasarsa don zuba jari.

Ya ce kasar Portugal tana goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya", tana kuma son zama babbar tasha ta hanyar siliki ta kasa, da hanyar siliki ta ruwa a yankin Turai. Kaza lika kasashen Sin da Portugal suna da matsayi guda kan harkokin kasa da kasa da dama, kuma dukkansu suna son kara hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, kuma suna goyon bayan 'yancin ciniki, yayin da suke adawa da kariyar ciniki, shi ya sa, ya kamata kasashen biyu su karfafa mu'amalar dake tsakaninsu cikin hukumomin dake shafar bangarori daban daban. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China