in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da takwaransa na Panama sun kai ziyara a sabon kuban jiragen ruwan na hanyar ruwan Panama
2018-12-04 11:17:30 cri
Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Panama Juan Carlos Varela sun kai ziyara a sabon kuban jiragen ruwa na hanyar ruwa ta Panama.

A lokacin, wani jirgin ruwa mai dauke da kayayyaki na kamfanin zirga-zirgar jiragen ruwa na COSCO na kasar Sin yana jira a kuba na farko domin shigewa. Wannan jirgin ruwa ya tashi ne daga birnin Qingdao na kasar Sin a ranar 1 ga watan Oktoba, wanda ya ketare tekun Pacific, da hanyar ruwa ta Panama, sa'an nan, ya isa tashoshin jiragen ruwa guda 3 na kasar Amurka ta tekun Atlantic, yanzu yana kan hanyar dawowa kasar Sin ta hanyar ruwan Panama.

Shugabannin biyu sun kai ziyara ofishin gudanar da ayyuka, inda shugaba Varela ya gayyaci shugaba Xi da ya bude kuban, domin jirgin ruwan ya ketare.

Hanyar ruwa ta Panama wata muhimmiya ce da ta hada tekun Pacific da tekun Atlantic, wadda ta fara aiki a shekarar 1914 a hukumance. Sa'an nan, a shekarar 1999, kasar Panama ta dawo da ikon gudanar da ayyyukan hanyar ruwan hannunta. A shekarar 2016 kuma, aka kammala aikin habaka hanyar ruwan ta Panama. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China