A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana son yin kokari tare da kasar Panama, wajen sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa tushen ka'idar Sin daya tak, ya kuma yi imanin cewa, za a kiyaye hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu har abada.
A nata bangare, Ábrego ta bayyana cewa, jam'iyyun kasar Panama sun cimma daidaito, da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Panama da Sin, wanda hakan ya samar da dama ga hadin gwiwar kasashen biyu. Ta ce majalissar dokokin jama'ar kasar Panama tana son kara yin mu'amala tare da kasar Sin, wajen samar da gudummawar inganta hadin gwiwarsu, da sada zumunta a tsakaninsu. (Zainab)