in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta ayyana 24 ga Janairu a matsayin ranar ilmi ta kasa da kasa
2018-12-04 10:03:35 cri

Babban taron MDD (UNGA) na ranar Litinin ya amince tare da ayyana ranar 24 ga watan Janairu a matsayin ranar ilmi ta kasa da kasa.

A yayin cikakken zama na 44 na babban taron MDD karo na 73, an gayyaci dukkannin kasashe mambobin MDD, da hukumomin kasa da kasa, da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi amfani da wannan rana, kuma ko wane bangare ya gudanar da bikin na wannan rana domin ba da gudunmowa wajen cimma nasarar ci gaban ilmi.

"Ilmi muhimmin ginshike ne wajen tabbatar da ci gaban duniya, kuma yana da muhimmanci a girmama wannan rana," in ji Tijjani Bande, wakilin din din din na Najeriya a MDD, ya kara da cewa, za'a yi amfani da wannan rana wajen neman goyon bayan mambobin kasashe domin su bunkasa tsarin samar da ilmi ga dukkan bil adama.

Ya bukaci al'ummomin duniya da su yi amfani da ranar ilimi ta MDDr da aka kebe, kana su kara samar da damammakin ilmi ga al'ummomi marasa galihu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China