in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu manyan nasarori a wajen taron kolin G20
2018-12-03 20:26:10 cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Litinin cewa, an samu dimbin nasarori a taron kolin G20 wanda aka kammala kwanan baya a kasar Argentina, al'amarin da ya kara sanya kuzari gami da karfafa gwiwar kasuwannin duniya.

Kasar Sin ta yi imanin cewa, muddin kasashe membobin kungiyar G20 su ka yi shawawari da juna sa'an nan su ka cimma ra'ayi daya, da daukar nauyin dake wuyansu bisa ra'ayin raya makomar bil'adama ta bai daya, da kuma karfafa hadin-gwiwa tsakaninsu, ko shakka babu za su bayar da karin gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya da kyautatuwar zaman rayuwar al'ummomin duniya. Kasar Sin ita ma za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China