in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na Sin ya yi bayani kan taron kolin shugabannin G20 karo na 13
2018-12-03 10:34:20 cri

Manzon musamman kan harkokin G20, kuma shugaban hukumar tattalin arzikin kasa da kasa ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Xiaolong, ya yi bayani kan taron kolin shugabannin rukunin G20 karo na 13, wanda ya samu halartar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Buenos Aires, fadar mulkin kasar Agentina a ranar 1 ga wata.

Wang Xiaolong ya bayyana cewa, an gudanar da taron kolin ne karkashin yanayi mai sarkakiya, wato tsarin kasashen duniya yana yin manyan sauye-sauye, haka kuma ana fama da matsalar ba da kariya ga harkokin cinikayya, da matsalar gudanar da cinikayya bisa gefe guda, ban da haka, ci gaban tattalin arzikin duniya yana fuskantar damammaki da kalubale tare, a don haka shugabannin kasashe mambobin rukunin G20 da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, sun yi tattaunawa kan muhimman batutuwan dake shafar tattalin arzikin duniya a yayin taron, daga baya sun fitar da "sanarwar taron kolin Buenos Aires na shugabannin G20", inda suka nuna wa al'ummomin kasa da kasa cewa, rukunin yana ci gaba da taka muhimmiyar rawa yayin da ake kokarin gudanar da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen duniya, gwamnatin kasar Sin ta taya masu shirya taron kolin murnar cikakkiyar nasarar da suka samu, a sa'i daya kuma ta nuna babban yabo gare su saboda kokarin da suke yi.

Hakika kasar Sin ita ma ta mai da hankali matuka kan taron kolin, kuma ta ba da gudummowarta. Bana ake cika shekaru goma da fara gudanar da taron kolin G20, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shiga taron ne har sau shida. Yayin taron da aka kira, shugaba Xi ya halarci taron rufe kofa na shugabannin, kuma ya shiga tattaunawar da aka yi bisa matakai uku, har ya ma gabatar da muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya takaita fasahohin da aka samu a fannin hadin gwiwar dake tsakanin mambobin G20, tun bayan da aka gamu da rikicin harkar kudi a fadin duniya, haka kuma ya gabatar da shawara game da nacewa ga manufar bude kofa da hadin gwiwa, tare kuma da kiyaye tsarin gudanar da cinikayya tsakanin bangarori daban daban, kana ya jaddada cewa, ya kamata a kara mai da hankali kan alakar abokantaka da sulhunta manufofi bisa manyan tsare-tsare, da kirkire-kirkire domin samun moriyar juna, tare kuma da cimma burin ingiza ci gaban kasa da kasa bisa tushen yin hakuri da juna, duk wadannan ra'ayoyin da shugaba Xi ya nuna sun samu karbuwa, da yabawa daga wajen shugabannin kasashe mambobin rukunin, wadanda suka halarci taron kolin.

Yayin taron, wakilan kasar Sin sun shiga tattaunawar da aka shirya, haka kuma sun ba da gudummowarsu ga cikakkiyar nasarar kammalar taron, ana iya ganin kokarinsu a fannoni hudu:

Na farko, ingiza cimma burin kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya dake tsakanin bangarori daban daban, da gyaran fuskar kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO. Kasar Sin ta bayyana cewa, dole ne a tabbatar da hakkin halal kanta, a don haka ba a rubuta abun da zai gurgunta moriyar kasar Sin a cikin sanarwar taron kolin da aka fitar, kana kasar Sin ta nuna goyon bayanta kan gyaran fuskar da kungiyar cinikin duniya take yi, domin kara kyautata aikinta, inda ta jaddada cewa, yayin da kungiyar take yin kwaskwarima, ya zama wajibi a kiyaye tsarin gudanar da harkokin cinikayya tsakanin bangarori daban daban, da ka'idojojin kungiyar, da kuma damammakin ci gaba na kasashe masu tasowa.

Na biyu, kasar Sin ta ba da jagoranci ga ci gaban tattalin arzikin duniya, an fitar da sanarwar taron kolin G20 na bana, lamarin da ya nuna cewa, kasashen duniya suna son warware sabanin da suke fuskanta, haka kuma suna son dakile kalubalen dake gabansu ta hanyar yin shawarwari.

Na uku, kasar Sin ta gabatar da shirinta na kyautata aikin gudanar da harkokin kasashen duniya, a karkashin kokarin da kasar Sin take yi, an sake bayyana cewa, za a tabbatar da muradun samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 da aka cimma, yayin taron kolin da aka gudanar a birnin Hangzhou na kasar Sin.

Na hudu, kasar Sin ta nuna niyyarta ta dakile matsalar sauyin yanayi, shugaba Xi ya sake nanatawa a cikin jawabinsa cewa, kasar Sin za ta cika alkawarin da ta yi kan batun.

Hakazalika, mamzon musamman na kasar Sin Wang Xiaolong ya bayyana cewa, yayin taron kolin, shugaba Xi ya halarci kwarya-kwaryar taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar BRICS, inda ya jaddada cewa, ya kamata kasashen BRICS su kara hada kansu, domin cimma burin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, da wadata a fadin duniya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China