A cikin sakon, Xi Jinping, ya bayyana marigayi Bush a matsayin tsohon aminin al'ummar kasar Sin wanda ya shaida tare da karfafa dangantaka tsakanin Sin da Amurka cikin shekaru 40 da suka gabata. Haka zalika, ya bada gudunmuwa ga abotar dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu, wadda al'ummar Sinawa ba za su manta ba.
Ya jaddada cewa, cikin lokaci mai tsawo, hulda tsakanin kasar Sin da Amurka ta yi ta ingantauwa bisa kokarin shugabanni da jama'ar kasashen, al'amarin da ya haifar da moriya ga jama'arsu da ma na sauran sassan duniya.
Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin ta na ba huldar dake tsakaninta da Amurka muhimmanci, kuma a shirye take ta inganta dangantakarsu bisa tafarkin da ya dace. (Fa'iza Mustapha)