in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Shugabannin kasashen Sin da Amurka na kokarin sassanta takaddamar cinikayya dake tsakaninsu
2018-12-02 17:29:15 cri
Takaddamar cinikayyar da ta shafe watanni takwas tsakanin kasashen Sin da Amurka na fuskantar wata muhimmiyar damar canjawa a daidai wannan lokaci, wato karshen shekarar 2018.

Shugaba Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, sun yi shawarwari a jiya 1 ga wata a kasar Argentina, karon farko ke nan da shugabannin biyu suka gana, bayan da takaddamar cinikayya ta tsananta tsakaninsu tun watan Maris din bana. Shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka jibanci tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka tare kuma da cimma maslaha a kansu, inda suka kuduri aniyar dakatar da daukar matakan kayyade cinikayya ciki har da kara sanyawa juna kudin haraji, da lalibo bakin zaren daidaita matsalolin cinikayyarsu ba tare da wani jinkiri ba. Shugabannin biyu sun kuma bukaci tawagogin jami'an tattalin arziki da cinikayyar kasashensu da su gaggauta yin shawarwari tsakaninsu, da cimma yarjejeniya, a wani kokari na maido da dangantakar tattalin arziki da cinikayyarsu bisa turba madaidaiciya, don cimma moriya tare.

Shugabannin Sin da Amurka na nan na kokarin sassanta takaddamar cinikayyarsu a daidai wannan lokaci na bayyana niyyarsu ta yin hadin-gwiwa don magance matsaloli. Har wa yau, al'amarin ya bayyana matsayi gami da manufofin gwamnatin kasar Sin na kiyaye babbar moriyar kasar gami da hakkokin jama'arta.

A wajen taron kolin kasashen kungiyar APEC wanda aka yi kwanan baya a kasar Papua New Guinea, shugaba Xi ya ce, babu wata kasar da za ta iya cimma nasara a yakin cacar baka ko na cinikayya, ko kuma a sauran yake-yake na zubar da jini. Takaddamar cinikayyar da aka shafe tsawon watanni takwas ana yi ta haifar da munanan illoli, al'amarin da ya tabbatar da irin wannan furuci na shugaba Xi, wato ba Sin da Amurka ne kawai suka yi hasara ba, domin akwai yiwuwar saurin karuwar cinikin hajjojin kasa da kasa a bana ya ragu da kashi 0.3 bisa dari, kuma asusun bada lamuni na duniya IMF a takaice ya rage hasashen karuwar tattalin arzikin duniya na bana da na badi daga kashi 3.9 bisa dari a watan Afrilun bana zuwa kashi 3.7 bisa dari a halin yanzu.

A irin wannan yanayin da ake ciki, shugaba Xi Jinping ya tattauna tare da shugaba Trump ta waya a watan Mayu da kuma na Nuwanba, ga shi kuma a wannan wata, sun gana da juna, kuma tuntubar juna a tsakaninsu ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsalar tattalin arziki da cinikayya a tsakaninsu.

A yayin da kasa da kasa ke kara dunkulewa da juna, yadda kasar Sin da Amurka suka kawo karshen takaddamar ciniki a tsakaninsu, babu shakka zai kawo babban alfanu ga kamfanoni da al'ummomin kasashen biyu, har ma da na duniya baki daya. An lura cewa, a gun bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na farko da aka gudanar ba da jimawa ba, kamfanonin kasar Amurka kimanin 180 ne suka hallara, adadin shi ne kaso daya daga cikin uku na kamfanonin kasar Japan da suka halarci bikin, kuma babban dalili shi ne illar da takaddamar ciniki a tsakanin Sin da Amurka ta haifar ga kamfanonin Amurka da ke fitar da kayayyakinsu ga kasar Sin.

Bisa ga daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma, an ce, bisa ga bukatunta na gida, kasar Sin za ta kara shigo da kayayyaki daga kasar Amurka a fannonin noma da makamashi da kayayyakin da aka sararfa da hidimomi da sauransu, ta yadda za ta kara biyan bukatun al'ummarta da jin dadin rayuwarsu da kuma kara inganta bunkasuwar tattalin arzikinta. A hakika, Sin da Amurka na taimakawa juna sosai a wadannan fannoni, don haka, kara shigo da kayayyakin Amurka ta wadannan fannoni, zai taimaka ga bunkasa harkokin cinikayya a tsakanin kasashen biyu cikin daidaito. Daga nata bangare kuma, kasar Amurka ma za ta yi kokarin daidaita matsalolin da ke jan hankalin kasar Sin, misali za ta maido da shigo da dafaffen naman kaji da makamantansu daga kasar Sin.

"Ko makomar na da haske ko akasinsa, gudanar da hadin kai da neman samun moriyar juna da samun nasara tare, shi ne zabi mafi dacewa daya kacal." Wannan ne tabbacin da shugaba Xi Jinping ya bayar a gun taron kolin G20 da aka shirya a Argentina, shi ne kuma ra'ayi da kuma hanyar da kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su bi wajen tinkarar takaddamar tattalin arziki da cinikayya dake akwai a tsakaninsu.

Bisa ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tawagogin kasashen biyu za su yi shawarwari na sabon zagaye. Kamar yadda ta kan yi a da, kasar Sin za ta ci gaba da la'akari da kiyaye moriyar bai daya ta kasashen biyu, da tsarin cinikayyar duniya, a yayin da take gabatar da hakikanin shirin warware matsaloli. A sa'i guda kuma, matsalolin tattalin arziki da cinikayya dake kasancewa a tsakanin kasashen biyu na da sarkakiya, don haka ba zai yiwu a warware dukkan matsalolin ta hanyar yin shawarwari na wasu zagaye ba, watakila ma za a yi karantsaye a yunkurin warware matsalolin. A don haka, kasar Sin za ta tsayawa matsayin da take dauka na tinkarar duk matsalolin da za ta fuskanta, saboda babu wani kalubale da zai iya hargitsa tattalin arzikinta.(Murtala Zhang, Lubabatu Lei, Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China