in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata a ci gaba da karfafa aikin yin rigakafi kan cutar kanjamau
2018-12-01 21:18:49 cri
Yau ranar 1 ga watan Disamba, rana ta kasa da kasa da aka ware don cutar kanjamau karo na 31, babban taken wannan rana a bana shi ne "Sanin matsayinka game da cutar". A jiya Jumma'a, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, shekaru 30 ke nan da ware wannan rana domin cutar kanjamau, sai dai har zuwa yanzu, daukar matakan riga kafi da kuma kulawa da masu cutar, ya kasance wani muhimmin aiki mai nauyi da ake fuskanta.

Wata sanarwa da ya fitar, ta ce ya zuwa yanzu, akwai mutane sama da miliyan 77 da suka kamu da kwayoyin cutar kanjamau, wato HIV, kuma mutane sama da miliyan 35 sun rasa rayukansu sakamakon cututukan da suke da nasaba da cutar kanjamau. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China