in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da takwaransa na Rasha
2018-12-01 16:47:21 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Buenos Aires, fadar mulkin kasar Argentina.

Yayin ganawar tasu, Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata su maimaita tarihin ziyarar juna ta shekara-shekara a tsakaninsu. Kuma ya yi imanin cewa, bisa jagorancin shugabannin biyu, huldar dake tsakanin kasashensu za ta bunkasa cikin yanayi mai kyau. Ya ce a nan gaba kuma, ya kamata su karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Turai da Asiya bisa shawarar Ziri daya da hanya daya, domin zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya da sha'anin kudi da makamashi da kuma kimiyya da fasaha da dai sauransu. Shugaba Xi ya kara da cewa, ya kamata a kyautata tsarin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Rasha domin raya dangantakar dake tsakanin wurare daban daban na kasashen biyu yadda ya kamata. Har ila yau, ya ce ya kamata kasashen biyu su sa kaimi ga sassa daban daban na kungiyar G20 da kasashen BRICS, da su kiyaye tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa da kuma kiyaye manufofi da ka'idojin hukumar WTO, domin goyon bayan 'yancin ciniki da nuna adawa da kariya.

A nasa bangaren, shugaba Putin ya ce, Rasha tana tsayawa tsayin daka wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin bisa fannoni daban daban, da kuma samar da gudummawa wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, da kiyaye tsarin ciniki mai bude kofa ga waje. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China