in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharihi: Yayin da 'yan siyasa na kasashe daban daban suke hallara a taron G20
2018-11-30 17:16:26 cri

"Taron koli na kungiyar G20 wani abu ne mafi muhimmanci a tarihin kasar Argentina."

"Shugabannin manyan kasashe sun taru a wata kasa dake bangon duniya, wannan abu ne mai ban sha'awa matuka."

"Mu 'yan Argentina muna son bayyana abubuwan misali mai alaka da alkaluma. Bari in gaya maka, kashi 80% na al'ummar Argentina sun yarda da gudanar da taron G20 a Buenos Aires, yayin da wadanda ke zanga-zanga a titi kalilan ne."

"Argentina ta bude kofarta, kuma za ta iya hakuri da ra'ayoyi daban daban. Ta la'akari da matsayin da kasar ta dauka na zama 'yan ba ruwanmu, gudanar da taron G20 a wannan kasa, wata dama ce mai kyau ga duniya."

'Yan Argentina da aka gamu da su a Buenos Aires sun bayyana ra'ayoyinsu dangane da taron G20 kamar haka.

Taron koli na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki G20 da za a kaddamar da a Buenos Aires a wannan Jumma'ar, shi ne karon farko da za a gudanar da irin wannan taro a wata kasar dake nahiyar Amurka ta Kudu. Kasar Argentina dake karbar bakuncin taron ta tsara wani tambarin taro mai ban sha'awa, wanda bai shafi wasu abubuwan da za su iya wakiltar kasar Argentina ba, maimakon haka ya kunshi wasu da'irori masu launuka daban daban. Kananan da'irori 20 dake waje na wakiltar kasashe mambobin kungiyar 20, sauran da'irori 5 dake yaduwa daga tsakiya zuwa waje suna madadin nahiyoyi 2 na duniya. Sa'an nan za a iya ganin da'irori 100 masu launuka daban daban a cikin tambarin, wadanda ke nufin duniya za ta kara dunkulewa waje guda, kana a wajen taron za a tattauna batutuwa daban daban.

Argentina kasa ce da aka fi sani da kasar rumbun hatsi da nama ta duniya, tana son nuna matsayinta ga 'yan siyasa da kafofin watsa labarai na kasa da kasa cewa, a lokacin nan na musamman da ake gamuwa da matsalar raya tattalin arzikin duniya, ya kamata 'yan siyasar kasa da kasa su maimaita burinsu wajen kafa taron kolin kungiyar G20 a farkon lokaci. Ta yaya za a samar da tabbaci ga al'ummomin kasa da kasa? Ta hanyar daidaita manufofin tattalin arzikin duniya a yayin taron kolin kungiyar 20, wani muhimmin dandalin hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa. Ya kamata mu karfafa hadin gwiwa, mu kuma tsaya tsayin daka wajen bude kofa ga waje domin samun ci gaba tare.

Kuma za mu gane wannan daga manyan jigogin da aka tsara a yayin taron na wannan karo, wadanda suka hada da "tattalin arzikin duniya", "cinikayya da zuba jari", "tattalin arziki na intanet", "dauwamammen ci gaba", "ababen more rayuwa" da kuma "sauyin yanayi", dukkansu ba sabbin jigogi ba ne. Amma, yanzu, an mai da wadannan jigogi sabuwar ma'ana sabo da matsalolin kariyar ciniki da adawa da tsarin ciniki dake tsakanin kasa da kasa da ake gamuwa da su a shekarar bana. Ya kamata 'yan siyasa su yi kira da a kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata, da kuma nuna goyon baya kan 'yancin ciniki, ta yadda za a iya gina wani tsarin ciniki mai bude kofa ga waje cikin hadin gwiwar gamayyar kasa da kasa.

A kwanakin baya, a kan samu sakon yin kashedi daga bangarori daban daban. Asusun IMF ya rage hasashen bunkasuwar tattalin arzikin duniya na shekarar bana da ta badi da kashi 0.2 cikin dari zuwa kashi 3.7 cikin dari. Wannan ne karo na farko da asusun IMF ya rage wannan hasashen tun bayan watan Yulin shekarar 2016. Ana iya ganin cewa, rikicin ciniki da mawuyacin hali na sabbin kasuwanci da raguwar saurin bunkasuwar yankin mai amfani da kudin Euro da sauransu, sun haddasa makoma mara haske ga tattalin arzikin duniya a halin yanzu. Yawan tattalin arzikin kasar Jamus na watan Yuli zuwa Satumba ya ragu da kashi 0.2 cikin dari. Masanan tattalin arziki da dama sun yi tsammanin cewa, wannan ya shaida alamar gama bunkasuwar tattalin arzikin yankin mai amfani da kudin Euro a shekaru 5 a jere.

Yaya za a hana raguwar tattalin arzikin duniya? Shugabar asusun IMF Christine Lagarde tana fatan shugabannin kasashen kungiyar G20 za su sake yin hadin gwiwa a gun taron koli na Argentina, da magance bada kariya ga cinikayya da dakatar da karuwar kudin kwastam, domin bada kariya ga cinikayya zai sa dukkan masu amfani da manufar su ci tura a karshe. A ganinta, shugabannin suna da damar musamman ta kyautata tsarin ciniki na duniya. Ta bayyana haka ne domin wani rahoton bincike na asusun IMF ya ce, kara yin cinikin samar da hidima zai sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin kungiyar G20 da kashi 0.5 cikin dari, wato zai kai dala biliyan 350.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a ranar 28 ga wannan wata cewa, kiyaye yin ciniki cikin 'yanci da adalci ya tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Kwanan nan, al'ummar kasar Argentina na fatan halartar taron kolin G20 da shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai yi da kuma ziyarar da ya yi a kasar ta Argentina za su samar da dabarar kasar Sin wajen daidaita mawuyacin halin da tattalin arzikin duniya ke ciki, tare da habaka hadin gwiwar kasashen biyu ta fannoni daban daban.

"hadin kan wata kungiya zai rubanya kokarin da ake yi", kamar yadda shugaba Xi Jinping ya tsamo wannan karin magana na kasar Jamus a yayin taron kolin G20 da aka yi a bara a birnin Hamburg, don bayyana muhimmancin abota tsakanin mambobin kungiyar G20. A yayin da tattalin arzikin duniya ke fuskantar rashin tabbas, ba yadda za a yi illa dai 'yan siyasa su hada kan juna, don tabbatar da ci gaban juna da moriyar juna.

Ana kiran birnin Ushuaia da ke kudancin kasar Argentina da "birni da mafi yankin kudanci a duniya" da kuma "bangon duniya". A dab da fara taron kolin G20 a wannan birnin da ke bangon duniya, ana fatan kada 'yan siyasa su manta da manufar G20 ta "hadin kan juna da samun ci gaban juna." (Bello,Maryam, Zainab, Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China