in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna bidiyo mai taken "karin maganar da shugaba Xi Jinping ya kan yi amfani da su"
2018-11-30 10:38:19 cri

Kafin shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli na kungiyar G20 tare da ziyartar kasar Argentina, an gabatar da wani bidiyo mai taken "karin maganar da shugaba Xi Jinping ya yi amfani da su a cikin jawabinsa" cikin harshen Spaniyanci a dukkan kasashe dake magana da harshen Spaniyanci a ranar 29 ga wata. A wannan rana, an gudanar da bikin nuna bidiyon a birnin Buenos Aires dake kasar Argentina.

Manyan kafofin watsa labaru na kasashen Argentina da Spaniya da sauran kasashe masu amfani da harshen Spaniyanci za su watsa wannan bidiyo, kana za a wallafa shi a shafin internet na manyan kungiyoyin masana masu amfani da harshen Spaniyanci kamar cibiyar nazarin batutuwan siyasa da tattalin arziki ta kasar Argentina. Haka kuma, babban gidan talabijin da rediyo na kasar Sin CMG zai watsa wannan bidiyo ta kafofinta daban daban.

Rahotanni na cewa, bidiyon yana kunshe da karin magana na gargajiya da shugaba Xi Jinping ya yi kan amfani da su a cikin jawabai da bayanai da ma maganganun da ya yi kana yana kunshe da fannonin bauta wa jama'a, dabi'a, gyara halaye, iyalai, girmama tsofaffi, gudanar da ayyuka ba tare da cin hanci da rashawa ba da dai sauransu, wadanda suka shaida cewa shugaba Xi Jinping ya fahimci al'adun gargajiya na kasar Sin sosai da koyon dabarun tafiyar da harkokin siyasa daga cikinsu.

A gun bikin gabatar da bidiyon, shugaban babban gidan telebijin da rediyo na kasar Sin CMG Mr Shen Haixiong ya bayyana cewa, wannan bidiyo da aka tsara cikin harshen Spaniyanci ya samar da dama ga masu kallo ta kara sanin shugaba Xi Jinping, da kuma yadda shugaba Xi Jinping ya jagoranci kasar Sin da raya kasar da yin kokarin cimma burin al'ummar kasar Sin.

Mutumin da ya kafa kungiyar kafofin watsa labaru na nahiyar Amurka Jose Luis Manzano ya bayyana wa 'yan jarida cewa, 'yan kasar Argentina da kasar Sin dukkansu suna dora muhimmanci a kan iyalai. Akwai wani batu da aka tattauna a cikin bidiyon mai suna iyalai, yana ganin cewa al'ummomin kasashen biyu suna da ra'ayi iri daya a wannan fanni. Ya kara da cewa, bidiyon ya samar da kyakkyawar dama ga masu kallo na kara sanin al'adun kasar Sin. Al'adu da tunanin kasar Sin suna da muhimmanci matuka ga zamantakewar al'umma a halin yanzu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China