Ya ce, yanzu zamani ne na dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda, don haka ya kamata a yi kokarin kare tsarin cinikayya cikin 'yanci da kasancewar bangarori daban-daban.
Gao Feng ya ce, karuwar ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da ra'ayin kashin kai, sun haifar da rashin tabbas ga ci gaban tattalin arzikin duniya, lamarin dake bukatar hadin gwiwar dukkan bangarori.
Ya ce, kasar Sin na fatan hada kai da kasar Argetina da ma ragowar sassa wajen zurfafa alaka a fannonin cinikayya da zuba jari, da bude kofar kasuwanni da samar da sabbin damammakin bunkasuwa.
Bayanai na nuna cewa, alkaluman GDPn mambobin G20 ya kai kaso 86 cikin 100 na GDPn duniya, yayin da darajar cinikyayyarsu ta kai kimanin kaso 80 cikin 100 na darajar cinikayyar duniya baki daya.
A don haka, jami'in na kasar Sin ya ce kasarsa na fatan yin sahihiyar tattaunawa da dukkan mambobin kungiyar game da harkokin cinikayyar kasa da kasa da sauran batutuwa.(Ibrahim)