in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin da Rasha sun taya murnar budewar dandalin makamashi tsakanin kasashen 2
2018-11-29 19:25:59 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a yau Alhamis, sun aike da sakwannin taya murna ga taron dandalin kasuwanci a fannin makamashi, wanda aka bude a tsakanin bangarorin Sin da Rasha.

Cikin sakonsa, shugaba Xi na kasar Sin ya ce, hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Rasha a fannin makamashi ya haifar da alfanu sosai, wanda ya taimakawa raya tattalin arzikin kasashen 2. Ya ce kasar Sin na son yin kokari tare da bangaren Rasha, don habaka hadin gwiwar dake tsakanin bangarorin 2 a fannin makamashi.

A nasa bangare, shugaba Putin na kasar Rasha ya ce, yanzu ana ta samun ci gaba a fannin kyautata huldar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin, wadda ta shafi hadin gwiwar da ake yi a fannin manyan tsare-tsare. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China