in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Yadda ake kallon taron G20 daga gyefe
2018-11-29 16:09:12 cri

A gobe Jumma'a, za a kaddamar da taron koli na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G20 a kasar Argentina. Wannan taro zai kasance mafi muhimmanci da tasiri a duniya da aka gudanar cikin wannan shekara.

Yanzu tattalin arzikin duniya na fama da tafiyar hawainiya, kana ana kara samun haddura da yanayin rashin tabbas yayin da ake neman raya tattalin arziki. Ban da haka kuma, ra'ayoyi na radin kai, da kare kai, da kuma yunkuri na hana dunkulewar duniya, suna yiwa tsarin kasa da kasa barazana. Ta la'akarin da wannan yanayin da ake ciki, sassan duniya na dora muhimmanci kan taron G20 na wannan karo, inda ake jiran ganin ko tsarin taron koli na G20 zai sake yin amfani a fannonin daidaita ra'ayoyin kasashe daban daban, da jagorantar hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A cewar wata tashar yanar gizo ta Internet mai suna "Arabnews", wannan taro ka iya zama irinsa mafi muhimmanci, tun bayan taron da aka kira a shekarar 2009 a birnin London na kasar Birtaniya, inda aka tattauna dabarar daidaita rikicin hada-hadar kudi da ya addabi duk duniya.

Bisa nazarin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi, an ce, hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa mai karfi domin fuskantar "bala'in tattalin arziki" a shekarar 2008 ta kasance madubin da za a kalli wannan taro daga gyefe". Ma'ana, an manta dukkanin manyan burin da 'yan siyasa suka tsara cikin taron kolin G20 a lokacin.

Matsalar sha'anin kudin da ta auku a shekarar 2008 ta kasance kamar batun jiya, inda asusun ba da lamuni na IMF ya rage hasashen karuwar tattalin arzikin duniya daga kaso 3.8% zuwa kaso -1.3%. Kungiyar G20 ta kuma hada kan kasa da kasa domin daidaita tsarin kudi, ta yadda za a warware matsalar tattalin arzikin duniya. A sa'i daya kuma, ta nemi karin rancen kudi na dallar Amurka biliyan 235 daga bankin raya sassa daban daban da kuma hukumomin sha'anin kudi, lamarin da ya sa ta daga matsayinta zuwa babban dandalin tattaunawar hadin gwiwar tattalin arziki na kasa da kasa.

Dalilin da ya sa taron koli na G20 na wancan karo da wadanda suka gabace shi suka iya tinkarar matsalar kudi yadda ya kamata, shi ne sabo da matsayin wakilci da mambobin kungiyar ke da shi, ra'ayi bai daya da shugabannin kasashe mambobin suka cimma na "zama uwa daya uba daya", da ma daidaituwar manufofinsu bisa manyan tsare-tsare da matakan a zo a ganin da suka dauka wajen bude kofarsu da na yadda suka hada kansu. Kungiyar G20 ta hada da kasashe biyar masu wakilcin din-din-din a kwamitin sulhu na MDD, da kasashe mambobin kungiyar BRICS, da ma kasashe mambobin kungiyar G7. Hakan ya sa ake dauka cewa, muddin wadannan muhimman kasashe sun dauki mataki na bai daya, to babu matsalar da ba za a iya warware ta ba.

A matsayinta ta kasa mai tasowa mafi girma da ma mambar kungiyar G20, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a cikin wancan matsalar kudi ta duniya. Wato ta kiyaye ci gaban tattalin arzikinta, da ma kara karfin takararta ta hanyar yin kwaskwarima ga tsarin tattalin arzikinta, baya ga kara bude kofarta ga waje. Alal misali, tun daga watan Fabrairu na shekarar 2009, kasar Sin ta sayi hajoji da darajarsu ta zarce dala biliyan 2.2 a kasuwar Turai, a kokarin inganta harkokin cinikayya da zuba jari. Hakan ya sa yawan gudummawar da kasar Sin ta ba karuwar tattalin arzikin duniya ya wuce kashi 50 cikin dari a shekarar 2009.

A yayin jerin tarukan koli na G20 da aka shirya a baya, kullum kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen inganta da tsayawa kan ra'ayin alakar kasa da kasa, da raya dangantakar abokantaka, da kuma neman samun nasara a yunkurin hadin kai mai salon bude kofa. Tun daga shekarar 2013 har zuwa yanzu, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya halarci tarukan kolin kungiyar har sau 5 a jere.

A yayin wadannan tarukan koli guda 5, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ya kamata kasashe daban daban su bullo da tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, da nuna adawa da ra'ayin ba da kariya ga harkokin cinikayya da zuba jari. Baya ga haka, ya yi kira ga kasashe daban daban da su "ci gaba da karfafa ra'ayin yin cinikayyar duniya cikin 'yanci, da kiyaye tsarin cinikayya na bangarori da dama, da bullo da tsari mai daraja a duniya mai samar da moriya da nasara tare, da kuma samar da babbar kasuwar duniya".

Ko shakka babu, a cikin wadannan shekaru 10, shugabanni na sauran kasashe mambobin kungiyar G20 su ma sun gabatar da manufofi da shawarwari masu inganci.

Idan aka waiwayi jerin tarukan kolin na G20 da ma takensu a cikin shekarun nan 10, da kuma kalubalen da ke bukatar a fuskanta a yanzu haka, ana ganin cewa, akwai bukatar daukar hakikanan matakai na hadin kai da samun daidaito, da kuma wani ra'ayi na kulla dangantakar moriyar juna da samun nasara tare a yayin taron kolin da za a shirya a Argentina, idan aka kwatanta da wadanda aka shirya a baya.

Alkaluman kididdigar hukumar WTO sun nuna cewa, tun daga watan Mayu zuwa Oktoba na bana, an dauki matakan kayyade ciniki a tsakanin mambobin hukumar WTO guda 40, wadanda suka shafi cinikin da darajarsu ta kai dala biliyan 481, wannan ya kai matsayin koli tun bayan irin wannan kididdiga da aka yi a shekarar 2012.

Don haka, manazarta da dama sun nuna shakku kan ko ba za a samu wani sakamako ba a yayin taron koli na kungiyar G20 na Argentina kamar taron koli na G7 da aka gudanar a watan Yuni na bana da kuma kwarya-kwaryan taron shugabannin kungiyar APEC da aka gudanar a watan Nuwanba na bana.

Taron koli na kungiyar G20 wani tsari ne, ba maganin da zai daidaita dukkan matsaloli ba. A shekarar 2013, yayin da batun siyasa ya kawo matsala ga taron koli na kungiyar G20 na birnin Saint Petersburg, wasu kafofin watsa labaru sun yi nuni da cewa, yayin da ake gudanar da taron kolin, akwai bukatar shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 su sake yin hadin gwiwa. Abu ne mai ma'ana ko da yake su yi ganawa da kuma tattaunawa, domin idan aka kara fahimtar juna, za a kara rage aukuwar duk wani hadari da ke shirin kunno kai.

A halin yanzu, muna iya ganin cewa, wannan tsari ya dace da yanayin da duniya ke ciki.(Bello, Maryam, Kande, Bilkisu, Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China