in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin tana son hada kai tare da sauran kasashe domin raya tattalin arzikin albarkatun ruwa
2018-11-29 11:11:56 cri

A yammacin ranar Talata 27 ga wata, agogon birnin Nairobin kasar Kenya, cibiyar kula da bayanan teku ta ma'aikatar albarkatun halittun kasar Sin ta kira taro kan tattalin arzikin albarkatun ruwa a birnin, inda wakilan kasar Sin suka yi bayani kan yanayin tattalin arzikin albarkatun ruwan kasar ke ciki, da sakamakon da ta samu a fannin.

Kasar Sin babbar kasa ce mai arzikin albarkatun ruwan teku, bayan kokarin da ake yi a cikin shekaru 40 da suka gabata, kasar Sin ta samu babban ci gaban tattalin arzikin albarkatun ruwa.

Yayin taron da cibiyar kula da bayanan ruwan teku ta ma'aikatar albarkatun halittun kasar Sin ta kira a Nairobin Kenya a yammacin ranar 27 ga wata, agogon wurin, darektan cibiyar He Guangshun ya bayyana cewa, a shekarar 2017, adadin kudin shigar da kasar Sin ta samu daga tattalin arzikin albarkatun ruwan teku ya kai kudin Sin yuan biliyan 7800, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1149 da miliyan 500, haka kuma an samar da guraben aikin yi miliyan 36 da dubu 500, ana iya cewa, tattalin arzikin albarkatun ruwa yana taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arzikin kasar, darekta He Guangshun yana mai cewa, "Ana iya kara fahimtar ci gaban tattalin arzikin albarkatun ruwan kasar Sin daga kyautatuwar tsohun tsarinsa, wato kama kifi da sufurin kayayyaki kan teku, misali tun bayan da aka fara aiwatar da manufar yin gyaran fuska a gida da bude kofa ga ketare shekaru 40 da suka gabata, adadin abincin ruwan tekun da kasar Sin ke samarwa ya karu har ninki 10, kana sana'o'in da ake gudanarwa ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohin kimiyya sun ci gaba cikin sauri, misali magungunan sha da ake hadawa da abincin ruwan teku, da yadda ake amfani da ruwan teku a rayuwar yau da kullum, da makamashin da ake iya sabuntawa da ake samarwa ta hanyar yin amfani da ruwan teku, da kera na'urorin da ake amfani da su yayin da ake gudanar da ayyuka a kan teku da sauransu."

Darekta He ya kara da cewa, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, a kai a kai adadin kifin da ake kamawa a tekun dake kusa da kan iyaka ya ragu, a sa'i daya kuma, adadin abincin ruwan da ake kiwo a cikin teku ya karu, a bayyane tsohuwar sana'ar kamun kifin a teku ta samu sabon ci gaba. Kana a fannin samar da makamashi kan teku, an ce, a shekarar 2017, adadin wutar lantarkin da aka samar ta hanyar yin amfani da iskar dake kadawa a kan teku a kasar Sin ya kai kilowatt miliyan 1 da dubu 160, adadin da ya karu da kaso 96.61 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar 2016, darekta He yana ganin cewa, daga alkaluman da aka samu, an lura cewa, ba ma kawai kasar Sin ta yi kokari domin raya tattalin arzikin albarkatun ruwa ba, har ma tana yin kokari matuka domin dakile matsalar sauyin yanayi, tare kuma da tsimin makamashi.

Ban da haka kasar Sin tana yin kokari domin hada kai da sauran kasashen duniya wajen kara ingiza bunkasuwar tattalin arzikin albarkatun ruwa, darekta He ya yi mana bayani kan batun daga fannoni uku: "Na farko, gabatar da shirin hada kai kan ci gaban tattalin arizkin albarkatun ruwa bisa shawarar ziri daya da hanya daya a watan Yunin shekarar 2017, na biyu gabatar da shawarar kulla huldar abokantaka domin raya tattalin arzikin albarkatun ruwa, na uku, gudanar da hadin gwiwar tsakanin kasa da kasa a fannin raya tattalin arzikin albarktun ruwa."

Hakika. kokarin da kasar Sin take yi a wannan fannin ya samu yabo daga wajen sauran kasashen duniya, kafin wannan, babban sakataren kula da harkokin mulki Ababu Namwamba ya taba bayyanawa yayin da yake zantawa da manema labarai cewa, ya amince da tunanin kasar Sin na raya tattalin arzikin albarkatun ruwa sosai, yana fatan kasarsa za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin a fannin, yana mai cewa,. "Alakar bangarori biyu tsakanin kasar Sin da kasar Kenya ko tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka suna da babbar ma'ana, mun lura cewa, kasar Sin tana son tattaunawa da kasashen Afirka kan batun raya tattalin arzikin albarkatun ruwa, domin samar da wadata da guraben aikin yi ga al'ummomin sassan biyu, tare kuma da kyautata rayuwarsu, duk wadannan sun burge mu matuka, muna fatan za mu kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninmu a wannan fannin a nan gaba."(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China