in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Uwargida Peng Liyuan ta ziyarci babban dakin nuna wasan kwaikwayo na masarautar Spaniya
2018-11-29 10:45:44 cri

Jiya da safe ne, Madam Peng Liyuan, uwargidan shugaban kasar Sin Xi Jinping ta ziyarci babban dakin nuna wasan kwaikwayo na masarautar kasar Spaniya da ke tsakiyar birnin Madrid, babban birnin kasar, bisa rakiyar mai dakin sarkin Spaniya Letizia Ortiz Rocasolano.

Uwargida Peng Liyuan ta bayyana cewa, wasannin fasaha na kowa ne, harshe ne na bai daya na bil Adam. Ta ce Sin da Spaniya muhimman kasashe ne da suka samu ci gaba a wannan fanni. Ko da yaushe kwararru masu wasannin fasaha na kaunar juna da son koyi da juna. Babban dakin nuna wasan kwaikwayo na masarautar kasar Spaniya, da babban dakin nuna wasan kwaikwayo na kasar Sin, na da kyakkyawar danganakar hadin gwiwa, wadanda dukkansu suka samar da dandamali masu kyau ga masu wasannin fasaha. Ya kamata a ci gaba da ingiza cudanya da hadin gwiwar kasashen biyu a fannin wasannin fasaha, don dada fahimta da karfafa zumunci a tsakanin jama'ar kasashen biyu.

An kafa babban dakin ne a shekarar 1818, kuma an shigar da shi cikin kawancen dakunan nuna wasan kwaikwayo na kasa da kasa da ke hanyar siliki a shekarar 2016.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China