in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Amurka 3 sun mutu a sakamakon harin da aka kai a gabashin kasar Afghanistan
2018-11-28 13:38:42 cri
Rundunar sojojin kungiyar tsaron NATO dake kasar Afghanistan ta sanar a jiya cewa, wani harin bam da aka kai jihar Ghazni dake gabashin kasar Afghanistan ya haddasa mutuwar sojojin Amurka 3.

Sanarwar ta bayyana cewa, an kai harin ne a kusa da birnin Ghazni dake jihar Ghazni, baya sojoji 3 da suka mutu, harin ya kuma raunata sojojin Amurka 3 da wani dan kasuwan kasar Amurka. Yanzu ana yiwa wadanda suka jikkata magani.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana sunayen mutanen da suka mutu ko suka ji rauni da ma karin bayani game da harin bam din ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China