in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kaddamar da gangamin wayar da kai kan kundin tsarin mulki a karo na farko
2018-11-27 15:46:00 cri

A karon farko, kasar Sin za ta kaddamar da makon gangamin wayar da kai game da kundin tsarin mulkin kasa, daga ranar 2 zuwa 8 ga watan Disamba.

Sanarwar da aka fitar a hukumance, ta yi kira da wayar da kan Sinawa matasa sosai da ma al'umma baki daya, ciki har da kamfanoni da yankunan karkara da sassan gwamnati da yanar gizo, a wani yanayi da zai samu karbuwa sosai ga jama'a.

Makon gangamin wani bangare ne na gangamin wayar da kai da zai shafe tsawon wata guda domin ranar kundin tsarin mulkin kasar na ranar 4 ga watan Disamba.

A ranar 4 ga watan Disamban 1982 ne kasar Sin ta amince da kundin tsarin mulkin da take amfani da shi a yanzu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China