in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya fusata matuka game da harin da Boko Haram ta kai wa sojojin kasar
2018-11-26 10:52:26 cri

Jiya Lahadi agogon tarayyar Najeriya, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar da wani jawabi kan rasuwar sojojin kasar sakamakon wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai musu kwanan baya a jihar Bornon dake arewa maso gabashin kasar, inda ya yi alkawari cewa, zai dauki mataki nan take domin yaki da ayyukan ta'addanci, tare kuma da ba da tabbacin tsaron sojoji da ma al'ummun kasar baki daya.

A ranar 18 ga wata, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin sojojin Najeriya dake kauyen Melete na jihar Bornon dake kan iyaka da kasar Chadi, inda aka kashe a kalla sojojin kasar 40. A cikin wata sanarwa da rundumar sojojin kasar ta fitar a yammacin ranar 23 ga wata, agogon wurin, ta bayyana cewa, rundunar sojojin kasar tana cikin mawuyacin yanayi, inda ta gamu da matsala matuka yayin da take kokarin yakar 'yan ta'adda, amma ba ta bayyana adadin sojojin da suka rasa rayukansu ba, daga baya wani 'dan majalisar dattijai ya bayyana cewa, adadin ya kai 44.

Ya zuwa ranar 24 ga wata, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya nuna mamaki matuka har ma ya fusata matuka ga harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wa kauyen Melete, kana ya tabbatar da cewa, zai dauki mataki ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban ya kara da cewa, ba zai yiyu ba wani kwamandan sojojin kasa ya yi shiru yayin da ya ga 'yan ta'adda suka hai hari ga sojojin kasarsa, haka kuma zai samar da dukkannin goyon baya ga sojojin wadanda suke yakar 'yan ta'adda, ta yadda za su dakile barazanar cikin nasara.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, a cikin 'yan kwanaki masu zuwa, zai tattauna da manyan jami'an tsaron kasar kan matakan da za su dauka a nan gaba, inda ya yi nuni da cewa, yakar ta'addanci aiki ne dake bukatar hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Rahotanni daga kafofin watsa labaran kasar ta Najeriya suna cewa, shugaba Buhari ya riga ya tura ministan tsaron kasar Mansur Dan Ali zuwa N'Djamena, babban birnin kasar Chadi domin yin shawarwari da gwamnatin kasar kan yadda kasashen biyu za su hada kai domin dakile barazanar ta'addanci tare.

An kafa kungiyar Boko Haram ne a shekarar 2004, tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu, kungiyar take ta kai hare-hare a fadin kasar, musamman a yankin dake arewa maso gabashin kasar, wani lokaci kuma, ta kan kai hare-hare a wasu kasashen dake makwabtaka da Najeirya, kamar su Chadi da Nijar da Kamaru da sauransu, a sanadin haka, fararen hula da sojoji da dama suka rasa rayukansu, kana wasu al'ummun kasar sama da miliyan 2 suka rasa muhallansu.

A tsakan daren ranar 23 ga wata, mayaka wajen 50 ne suka yi garkuwa da 'yan mata 15 a Toumour, wani kauye a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar Jamhuriyar Nijar, a ranar 22 ga wata kuwa, mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane 8 a harabar wani kamfanin hakar man fetur na kasar Faransa a kauyen na Toumour.

Tun daga shekarar 2015 ne kungiyar Boko Haram ta sanar da yin mubaya'a ga kungiyar IS wato kasar Musulunci, kuma ta sanar da cewa, za ta mayar da hedkwatarta dake yammacin Afirka a matsayin kasar Musulunci.

Hakika a baya shugaba Buhari ya yi alkawari cewa, zai kawar da kungiyar Boko Haram kwata-kwata yayin da ya ke takarar neman kujerar shugaban kasar a shekarar 2015, haka kuma gwamnatinsa tana kokarin daukar matakan dakile ayyukan ta'addancin kungiyar a cikin shekaru 2 da suka gabata, inda ta yi nasara sake kwato wasu yankuna dake hannun mayakan kungiyar, amma har yanzu 'yan ta'addan Boko Haram suna ci gaba da kai hare-hare ga sojoji da al'ummun kasar.

Za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya a watan Fabrairun shekarar 2019 dake tafe, a don haka idan shugaba Buhari yana son yin tazarce a kasar, dole ya mai da hankali kan aikin dakile ta'addancin Boko Haram a yankin dake arewa maso gabashin kasar, a sa'i daya kuma, ya dace ya kara ba da muhimmanci kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen dake yankin tafkin Chadi domin kawar da ta'addanci a yankin baki daya.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China