in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kai karamin ofishin jakadancinta dake Karachin Pakistan
2018-11-23 20:15:17 cri

A yau ne ofishin jakadancin kasar Sin dake Pakistan ya tabbatar da cewa, an kai hari kan karamin ofishin jakadancin kasar ta Sin dake Karachi a kudancin kasar Pakistan, ya kuma yi Allah wadai da kakkausar murya kan wannan hari na ta'addanci. Sai dai kuma dukkan Sinawan dake harabar ofishin suna cikin koshin lafiya.

Sashen hulda da jama'a na bangaren sojojin Pakistan ya bayyana cewa, an damke dukkan 'yan ta'addan uku dake da hannu a wannan hare.

Shi ma firaministan Pakistan Imran Khan ya yi Allah wadai da harin, inda ya ba da umarni a gudanar da cikakken bincike game da lamarin, tare da gano da ma hukunta duk wadanda ke da hannu wajen kai wannan hari

Majiyar 'yan sanda na cewa, a kalla mutane bakwai ne, ciki har da 'yan sanda biyu da fararen hula biyu da 'yan ta'adda uku ne harin ya rutsa da su.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China