in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar wajen Sin: Sin ta yi Allah wadai da harin da ake kai wa ofisoshin diflomasiya
2018-11-23 20:11:37 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan duk wasu hare-haren da ake kai wa hukumomin diplomasiyya. Jami'in na bayyana hakan ne, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancin Sin dake birnin Karachi na kasar Pakistan

Jami'in ya kara da cewa, daukacin ma'aikatan dake aiki a karamin ofishin jadakanci da daukacin iyalansu suna cikin koshin lafiya a halin yanzu, kana gwamnatin kasar Sin ta nuna juyayi ga jami'an tsaron kasar Pakistan wadanda suka rasa rayukansu a yayin harin, haka kuma ta isar da sakon jaje ga iyalan jami'an tsaron da sauran wadanda suka ji rauni a harin.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China