in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan wajen Pakistan: Kasarsa za ta tabbatar da tsaron Sinawa
2018-11-23 20:05:07 cri

A yammacin yau ne mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya buga waya ga takwaransa na kasar Pakistan Shah Mehmood Qureshi cikin gaggawa, inda Qureshi ya yi masa bayani kan harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Karachi a wannan rana, kana ya gaya wa Wang sakamakon farko na binciken da hukumomin kasar suka gudanar, haka kuma ya bayyana cewa, gwamnati da bangarori daban daban na Pakistan sun yi suka da kakkausar murya kan harin da 'yan ta'adda suka yi, a sa'i daya kuma, ya jaddada cewa, Pakistan za ta ci gaba da gudanar da bincike kan harin, tare kuma da daukar dukkanin matakai da suka dace domin dakile barazanar ta'addanci daga duk fannoni.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce, gwamnatin kasar Sin ta yi mamaki matuka kan harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancinta dake Karachi, tana mai Allah wadai da wannan harin ta'addancin da aka kai karamin ofishin jakadancinta.

Ban da haka, Wang Yi ya bukaci Pakistan da ta kara mai da hankali kan lamarin, tare kuma da gudanar da cikakken bincike kan harin, domin hana sake aukuwar irinsa a nan gaba, Wang ya jaddada cewa, ba zai yiyu ba a lalata zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Pakistan, yana mai hakakan cewa, Pakistan tana kokarin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a cikin kasar.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China