in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bude kofa ga juna, kuma hadin gwiwa da juna
2018-11-23 16:07:18 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda bai dade da kammala ziyarar aiki a wasu kasashen Asiya da tekun Pasifik ba, zai fara ziyara a kasashen Spaniya, da Argentina, da Panama, da Portugal da sauransu a ranar Talata mai zuwa, tare da halartar taron shugabannin kungiyar G20 da za a gudanar a birnin Buenos Aires, babban birnin kasar Argentina.

Bana ake cika shekaru dari da kawo karshen yakin duniya na farko, haka kuma ake cika shekaru 10 da kawo karshen rikicin hada-hadar kudi a duniya wanda ya auku a shekarar 2008. Ban da haka, a shekarar, an sha fama da yadda ake kyamar dunkulewar duniya baki daya, da zartar da ra'ayi na kashin kai, da kuma kariyar ciniki.

A irin yanayin da ake ciki, ya kamata kasa da kasa su natsu tare da waiwayar baya, don su koyi darasi, da kuma samar da tabbas, da kuzari ga cimma kyakkyawar makoma. Yadda manyan shugabannin kasar Sin ke ta ziyara zuwa kasashen waje, ya bayyana niyyar kasar, da kuma kokarinta wajen samar da dabararta ta daidaita matsalolin da ake fuskanta, musamman a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma kasar da ke da kujerar din din din a kwamitin sulhun MDD.

A wannan ziyarar da shugaba Xi Jinping zai fara, kasashen Spaniya, da Argentina, da Panama, da Portugal, dukkaninsu sun gano hanyar yin hadin gwiwar cin moriyar juna da kasar Sin, bisa ga tsarin raya "ziri daya da hanya daya".

Alkaluman da aka samu sun nuna cewa, tun bayan da aka kaddamar da layin dogon da ya hade Yiwu na kasar Sin da Madrid na kasar Spaniya, wanda shi ne mafi tsawo a duniya, a watan Nuwanban shekarar 2014, yawan kayayyakin da kasar Spaniya ta fitar zuwa garin Yiwu ya karu sosai, inda kudin cinikin ya karu daga kasa da dalar Amurka miliyan 1.6 a shekarar 2014, zuwa fiye da dala miliyan 10 na shekarar 2017. Ta haka aka samu karin yawan nau'ikan kayayyakin da ake sayar da su a babbar kasuwar kananan kayayyaki ta garin Yiwu.

Zuwa yanzu, garin Yiwu ya kulla huldar ciniki da kasashe da yankuna 219, yayin da kaso 65% na tattalin arzikin wurin suka shafi kasashen ketare. A ko wacce shekara, a kan samu 'yan kasuwan kasashen waje fiye da dubu 800, wadanda suka shiga garin Yiwu domin sayen kaya, yayin da 'yan kasuwa baki fiye da 15000, wadanda ke wakiltar kasashe da yankuna fiye da 100, ke zama a garin domin gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

A wajen bikin sayen kayayyaki da aka gudanar da shi a kasar Sin a ranar 11 ga watan Nuwamban da muke ciki, gami da taron baje kolin kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su, naman shanu da yankin Pampeana na kasar Argentina ya samar ya samu karbuwa sosai, har ma wani kanti mai sayar da kaya kan yanar gizo ko Internet, ya samu sayar da gutsure 10000 na naman shanun cikin minti daya. A cewar jakadan kasar Argentina a kasar Sin Diego Ramiro Guelar, kasarsa tana fitar da dimbin naman shanu zuwa kasar Sin, wanda ya kai fiye da rabin naman shanun da kasar ke fitarwa zuwa kasashen waje. Ana hasashen cewa, kudin naman da kasar Argentina ke fitarwa zuwa kasar Sin cikin shekara daya zai kai dalar Amurka biliyan daya.

Kasar Panama wadda ta kulla dangantakar diplomasiyya tare da kasar Sin a shekarar bara, ita ce kasar Latin Amurka ta farko da ta daddale takardar fahimtar juna ta raya shawarar "ziri daya da hanya daya" tare da kasar Sin.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Panama Luis Miguel Hincapie, yana fatan yin amfani da fifikon kasarsa, wato tashar musayar kayayyaki da ciniki, ta haka za ta kasance kofa ko gada, wajen sa kaimi ga kasar Sin da ta shiga kasuwar Latin Amurka.

Kasar Portugal tana son kasancewa gada, wajen sa kaimi ga raya shawarar "ziri daya da hanya daya" a nahiyar Turai, da kuma hada yankin Afirka da yankin kudancin Amurka. A shekarar 2011, rikicin bashi na nahiyar Turai ya barke, kasa da kasa sun nuna rashin yin imani ga kasuwar kasar Portugal, da rage zuba jari ga kasar. Amma kamfanonin kasar Sin sun zuba jari da yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Portugal. Bisa kididdigar da aka yi, ya zuwa yanzu, yawan jarin da kamfanonin Sin suka zuba ga kasar Portugal ya kai fiye da kudin Euro biliyan 9, kasar Portugal ta riga ta kasance kasa ta biyar da Sin ta fi zubawa jari a nahiyar Turai. Game da wannan batu, ministan harkokin tattalin arzikin kasar Portugal Manuel Caldeira Cabral ya taba bayyana cewa, kamfanonin kasar Sin sun nuna imani ga tattalin arzikin kasar Portugal, da nuna goyon baya gare ta. Gwamnatin kasar Portugal ta nuna godiya gare su, wannan ne muhimmin aikin da ya taimaki kasar wajen kawar da mawuyacin hali.

A shekarar 2018, mun gamu da matsaloli da dama, gabanin zuwan shekarar 2019, ya kamata kasa da kasa su nuna fahimtar juna, da kuma yin hadin gwiwa domin neman makomarmu mai haske. Bisa rahoton da kwalejin nazarin harkokin tattalin arziki na jami'ar Oxford ta fidda a jiya Alhamis, an ce, a shekarar 2019 mai zuwa, adadin karuwar tattalin arzikin duniya zai ragu daga 3.1% na bana zuwa 2.8%. Shi ya sa, ya kamata shugabannin kungiyar G20, wadda gaba daya karfin GDPn su da na cinikayyar kasa da kasa ta su ya kai 85% da 75% bisa na kasashen duniya, su karfafa hadin gwiwa a tsakaninsu, domin kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin kasa da kasa, da kuma zurfafa hadin gwiwarsu bisa fannoni daban daban.

A yayin ziyarar sa a kasar Argentina, watakila shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da takwaransa na kasar Amurka Donald Trump, kuma wannan zai kasance ganawarsu ta farko bayan barkewar takaddamar cinikin dake tsakanin kasashen biyu. Kasashen Sin da Amurka su ne manyan kasashe masu samun saurin bunkasuwar tattalin arziki a nan duniya, yadda shugabannin kasashen biyu za su daidaita dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zai samar da muhimmin tasiri ga sassa daban daban, shi ya sa, kasashen duniya suna mai da hankali kwarai kan ganawar shugabannin biyu. Bayan kafuwar huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu, ya zuwa yanzu shekaru 40 sun riga suka gabata, kuma wani muhimmin darasin da muka koyo cikin wadannan shekaru shi ne, yin hadin gwiwa zai tabbatar da nasarori na bangarorin biyu, yayin da sabanin zai haddasa hasararsu. (Lubabatu Lei, Bello Wang, Zainab Zhang, Maryam Yang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China