in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya yi barazanar rufe daukacin kan iyakar kasar sa da Mexico
2018-11-23 11:07:23 cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya sake yin barazanar rufe daukacin kan iyakokin Amurka da kasar Mexico, a wani mataki da gwamnatin sa ke dauka, na dakile kwararar bakin haure daga yankuna nahiyar tsakiyar Amurka zuwa cikin kasar sa. Tuni dai aka jibge dubban dakarun sojin Amurka a yankunan kan iyakar kasar ta kudanci, domin karfafa tsaron iyakar da kasar Mexico, inda sojojin ke tallafawa ayyukan injiniya, da tsare tsare, da hidimomin lafiya. Sai dai kuma a jiya Alhamis, shugaba Trump ya ce ya baiwa sojojin umarnin amfani da karfi, wajen dakile shigar bakin hauren cikin Amurka a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Rahotanni na cewa, wasu gungun bakin haure sun yi kwamba, inda suka tunkari Amurka domin neman mafaka. An ce cikin su akwai wadanda ke neman mafaka bayan tserewa gallazawa a kasashen su, da wadanda kangin talauci, ko tashe tashen hankula suka rabo su da kasashen Honduras, da Guatemala, da El Salvador. Kawo yanzu dai sama da 1,000 daga cikin bakin hauren sun riga sun isa garin Tijuan dake kan iyakar kasar Mexico. (Saminu Alhassan)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China