in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya bukaci a shirya zaben Kongo Kinshasa yadda ya kamata
2018-11-22 16:27:47 cri
Jiya kwamitin sulhun MDD ya bayar da sanarwa ta kafofin watsa labaru, inda ya jaddada cewa, zaben kasar Kongo Kinshasa da za a shirya a ranar 23 ga wata mai zuwa, na da muhimmanci kwarai ga kasar, ya kuma bukaci bangarori daban daban da su tabbatar da shirya zaben cikin nasara.

Sanarwar ta ce, wannan zaben zai samar da dama ga kasar ta Kongo Kinshasa, wajen tabbatar da mika mulki cikin lumana, da inganta zaman karko na al'umma, da kuma neman ci gaban tattalin arziki. Don haka, ta yi kira ga jam'iyyu daban daban da masu goyon bayansu, da kuma sauran 'yan siyasa su bi tsarin mulkin kasar, da kuma yarjejeniyoyin siyasa da batun ya shafa, da kuma ajandar zaben a dukkan fannoni, don shiga aikin zaben ta hanyar lumana. Sanarwar ta kuma bukaci a tabbatar da tsaron 'yan takara da masu jefa kuri'a.

Baya ga haka, sanarwar ta bukaci da a kiyaye tsaron ma'aikatan MDD, da na masu sa ido, masu kiyaye zaman lafiya, da kwararru, don su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China