in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a yi hadin gwiwa wajen yaki da laifuka masu alaka da hallaka dabbobin daji
2018-11-22 10:40:58 cri
A jiya Laraba ne daraktan sashen UNODC dake yaki da fataucin miyagun kwayoyi da muggan laifuka, karkashin laimar MDD Miwa Panholzer Kato, ya bukaci a inganta hadin gwiwa, wajen yaki da laifuka masu alaka da hallaka dabbobin daji.

Miwa Panholzer Kato, ya shaidawa wani taron karawa juna sani a birnin Nairobin kasar Kenya cewa, ana aikata laifuka masu nasaba da hallaka dabbobin daji a boye, kuma laifi ne dake samar da riba mai tarin yawa ga masu aikata su, wanda kuma ke zama kalubale ga kasashe da al'ummu daban daban, a fannin inganta rayuwar halittun daji da tattalin arziki daga albarkatu.

Ya ce idan ana son a yaki matsalar kisa, ko fataucin dabbobin daji, ciki hadda wadanda ke bakin karewa daga ban kasa, to ya zama dole a kara azama wajen hadin gwiwar aiwatar da kudurorin nan, na wanzar da muradun ci gaba nan da shekarar 2030, musamman ma kudurori na 14 da 15.

Taron na yini uku, na gudana ne karkashin inuwar dandalin ICCWC, wanda ya hada wakilai daga MDD da ofishin UNODC, da hukumar Interpol, da hukumar kwastam ta kasa da kasa, da ofishin bankin duniya, da kuma ofishin hukumar CITES mai rajin kare halittu. Wannan ne dai karon farko da yake gudana a nahiyar Afirka.

Mahalarata taron sun kunshi jami'an kwastam, da masu gabatar da kara, da masu bincike a fannin hada hadar kudade daga kasashen Afirka da Asiya sama da 20. Ana kuma tattaunawa game da yadda kasashen Afirka da na Asiya za su inganta hadin gwiwa, wajen dakile laifuka masu nasaba da hallakawa, ko fataucin dabbobin daji ta hanyar shari'a. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China