in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Trump ya jaddada kyakkyawar alakar kasar sa da Saudiyya
2018-11-21 11:16:36 cri
Shugaban Amurka Donald Trump ya jaddada kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar sa da Saudiyya, matakin da wasu ke ganin ya sabawa akidun Amurka, duba da irin takaddamar da ta biyo bayan kisan dan jaridar nan dan asalin kasar Saudiyya Jamal Khashoggi, wanda ake zargin mahukuntan Saudiyyar da aikatawa.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar, ta ruwaito shugaba Trump na cewa, kasar sa za ta ci gaba da kare muradun masarautar Saudiyya, da muradun kasar Isra'ila, da ma sauran abokan kawancenta dake yankin Gabas ta Tsakiya.

Ya ce Saudiyya ta yi kawance da Amurka wajen kalubalantar Iran, kuma jarin da masarautar ta zuwa ga Amurka, biyowa bayan ziyarar da ya kai a bara, ya kai na dalar Amurka biliyan 450, ciki hadda cinikayyar makamai na dala biliyan 110, da ake fatan Saudiyyar za ta gudanar da wasu kamfanonin kasar Amurka.

To sai dai kuma jami'ai a White House sun ci gaba da kaucewa yin tsokaci, game da batun zargin da ake yiwa masarautar Saudiyyar da hannu cikin kisan dan jarida Khashoggi, wanda kisan na sa ya sha suka daga sassan kasa da kasa.

Khashoggi ya bace ne bayan da ya shiga karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Istambul na kasar Turkiyya, a ranar 2 ga watan Oktoba, inda daga bisani bayanai suka tabbatar da an hallaka shi, a cikin karamin ofishin jakadancin. Duk da bayanan da aka samu, Saudiyya ta nace cewa babu hannun mahukuntan kasar ta, illa dai fada ne ya barke tsakanin sa da wasu jami'ai, wanda hakan ya sabbaba rasuwar sa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China