in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin saman Amurka sun hallaka dakarun Al-Shabaab 37
2018-11-21 11:00:01 cri
Ofishin kwamandan rundunar sojojin Amurka da ke Afirka a jiya Talata ya bayar da sanarwa, inda ya ce, a hare-haren sama da sojojin rundunar kasarsa suka kaiwa kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Al-Shabaab a ranar 19 ga wata a tsakiyar kasar ta Somaliya, an hallaka dakarun kungiyar 37.

Sanarwar ta ce, sojojin Amurka sun hada gwiwa da sojojin gwamnatin Somaliya, wadanda suka kai hare-haren sama har sau biyu ga sansanin kungiyar al-Shabaab da ke tsakiyar kasar Somaliya.

Sanarwar ta kara da cewa, sojojin Amurka za ta ci gaba da hada gwiwa da tawagar musamman da tarayyar Afirka ta tura zuwa Somaliya, da kuma rundunar tsaro ta Somaliya don yakar 'yan ta'adda.

Kungiyar Al-shabaab, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ce da ke da nasaba da kungiyar al-Qaeda, wadda ta sha kai hare-hare a Somaliya, da ma kasashen da ke makwabtaka da ita. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China