in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Isra'ila ya karbe ragamar ma'aikatar tsaro
2018-11-19 13:56:23 cri
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya sanar a jiya Lahadi cewa, zai rike mukamin ministan tsaron kasar yayin da yake tsaka da kokarin kare gwamnatinsa daga rushewa.

A wani jawabi da aka yada ta kafofin watsa labarai daga hedkwatar tsaro ta kasar dake Tel Aviv, Benjamin Netanyahu, ya ce zai karbe ragamar ma'aikatar tsaron ne biyo bayan murabus din da ministan tsaro Avigdor Lieberman ya yi.

Benyamin Netanyahu ya ce yana dukkan kokarin ganin an magance takkadamar da ake yanzu cikin kawacen jam'iyyu, domin kaucewa zaben wuri.

Ya kuma soki ministocin da suka yi kira da gudanar da zaben wurin, bayan rinjayen kujera 1 tak da kawancen jam'iyyun ke da shi yanzu, yana mai cewa yanayin da ake ciki yanzu, ba zai bar kawancen ya yi aiki kamar yadda ya kamata ba.

Baya ga matsayin firaminista, Netanyahu na rike da ragamar ma'aikatar harkokin wajen kasar. A hukumance dai, za a gudanar da babban zaben Isra'ila ne a watan Nuwamban 2019. Amma idan aka kira zaben wuri, to za a iya gudanar da shi a watan Maris din 2019. (Fa'iza Msutapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China